Sanin makamar aiki na sa jama’a su samu wakilci nagari – Shugaban majalisar Jihar Kano

Shugaban majalisar  dokokin Jihar Kano, Alhaji  Kabir Alhassan Rorum ya halarci kwas din kwanaki 10  a Chicago dake  cikin Jihar Illinous da ke nan Amurka.  Kuma  wakilin Aminiya da ke Washington, Abubakar Ibrahim ya  samu  damar zantawa  da shi  kan wannan kwas  na kwanaki 10  da  ya yi  shi da  wasu  ’yan majalisun dokokin sauran […]

Sanin makamar aiki na sa jama’a su samu wakilci nagari – Shugaban majalisar Jihar Kano
Sanin makamar aiki na sa jama’a su samu wakilci nagari – Shugaban majalisar Jihar Kano

Shugaban majalisar  dokokin Jihar Kano, Alhaji  Kabir Alhassan Rorum ya halarci kwas din kwanaki 10  a Chicago dake  cikin Jihar Illinous da ke nan Amurka.  Kuma  wakilin Aminiya da ke Washington, Abubakar Ibrahim ya  samu  damar zantawa  da shi  kan wannan kwas  na kwanaki 10  da  ya yi  shi da  wasu  ’yan majalisun dokokin sauran kasashen duniya.Ga kuma yadda  hirar  ta kasance.

Aminiya: Da farko za mu so ka fada mana shin me ya kawo ku Chicago ne?
Alhaji Kabir Alhassan Rorum: Babban dalilin da ya kawo mu nan kasar Amurka a birnin Chicago, shi ne, halartar kwas na sanin makamar aiki da kuma tafiyar da ayyukan majalisa, wanda ake koya muna yanzu haka a nan jami’ar Chicago.
Aminiya: Abin da mutane za su ce shi ne, an rasa duk inda za a koyi makamar aiki da ayyukan majalisa sai an baro Najeriya zuwa Amurka.
Alhassan: Ka san duk dimokuradiyya ta duniya, musammam mu a Najeriya kasar da ake koyi da ita ce Amurka. Don haka hakikanin gaskiya yana da kyau a rinka zuwa ana karo ilmi game da wannan dimokuradiyya, tunda ko ba komai ai irin tsarin su muke bi, kuma su, sun dade da farawa, kuma ya zamanto cewa, ana wannan dimokuradiyyar domin mutanen da suka zabe mu su samu wakilci nigari, kuma wannan kwas da muke zuwa zai kara wa mutum ilmi game da ayyukan da yake yi. Duk ire-iren wadannan kwasa-kwasan da ’yan majalisu ke zuwa ko na jiha ko na tarayya zai kara musu basira domin su iya ba da wakilcin da ake sa ran su bayar, da wannan ake yin dokokin da suka dace, domin ci gaban kasa baki daya. Don haka zuwa nan Chicago ba wani abin da za a ce a yi surutu akan sa ba ne.Wannan ya kamata a ce ana yinsa lokaci-lokaci, domin ko wannan jami’ar ta kware wajen koyar da harkokin mulki, ba ga ’yan Najeriya kawai ba a’a duniya baki daya an san wannan jami’ar wajen horarwa game da sha’anin mulki.
Aminiya: To Honarabul wasu za su ce aikin ku shi ne sun hada da sa’ido ga ayyukan sashen zartarwa da kuma yin dokoki, amma sau tari ’yan Najeriya na kallon ku ne a matsayin ’yan amshin shata, saboda haka zuwa irin wannan kwas din tamkar barnar kudin talakka ne. Me za ka ce wa masu irin wannan tunani?
Alhassan: Na farko bai dace mutane su rika wannan tunanin ba, domin babban aikin ’yan majalisa shi ne, samar da dokoki na ci gaban kasa da al’umma dare da kare addini da al’adar wurin da kuke wa shugabanci, tare da duba yadda ake kashe kudaden al’umma, musamman ta bangaren manyan jami’an gwamnati, manya da kanana kuma kamar yadda ka fa fada da kuma idan ba su goge ba, ya ya za su samu basirar gudanar da dukkan wadannan ayyukan. Su mutane sau tari abin da suke so su ji, shi ne, su ji ana yawan kai ruwa rana. Sau tari irin bibiyar da ’yan majilisa ke yi na ayyukan bangaren zartarwa idan ’yan majalisa sun ga inda aka yi ba daidai ba, sukan tabbatar sun janyo hankalin gwamnati domin ta duba wannan abu kuma ta gyara.Haka suma wadanda aka bai wa kwangila ’yan majalisa kan kira su a kan duk wani aiki da aka ba su ake cewa, akwai bukatar su gyara, su kuma gyara idan nay abo ne kuma a yaba, amma ba wai sai anyi sa insa sa ba. Amma akasarin mutane suna muna mummunar fahimta cewa bamu abin da ya kamata a ce muna yi, mu kuma mun tabbatar muna iya bakin kokarin mu wajen ganin an kashe kudaden al’umma yadda ya kamata a kashe su musammam a karkashin jagoranci na a majilisar dokokin jihar Kano.
Aminiya: To Honarabul da yake kwas ba ku kadai ne ’yan Najeriya ke wannankwas din ba, ko akwai wani abu da kuka anfana da shi daga wurin wasu da kuka hadu da su a wannan kwas din, musammam akan abin da ya shafi aikin majalisa?
Alhassan: Alhamdulillahi kusan kullum akan ware awa daya zuwa biyu, musammam mu da muka fito daga kasashen Afirka, musammam mu a Najeriya, za a hada da yan majilisun da suka fito daga kasashen gabashin Turai ko tsakiyar Turai ka ga ni muna kwamiti guda ne da shugaban majalisar dokokin Australiya da kuma wasu ’yan majilisar dokokin nan Amurka, a wannan kwamitin muna musayar ra’ayi ne game da yadda kowa ke tafiyar da harkokin majalisar sa, kuma hakan ya kara muna wata basira duk da yake sun riga mu farawa suna da yancin damu bamu da shi domin su yan majalisun kasashen nan suna cin gashin kansu ne, sabanin irin tsarin mu, wanda ya dogara ga bangaren zartarwa duk abin da ya taso maka sai majalisar zartarwa ta baka tallafi sabanin kasashen da suka ci gaba ’yan majilisa suna cin gashin kansu ne.
Aminiya: To mene ne fatar ka Honarabul game da wannan kwas, musammam ganin cewa, kuma kun samu irin wannan ’yancin kuma ba ma majalisar dokokin Jihar Kano kawai ba, a’a, Najeriya baki daya?
Alhassan: Fata na farko, shi ne, tunda yanzu an samu sabon shugaban kasa mai son canji, kuma mai son abi doka da oda, wato mai girma Shugaba Muhammadu Buhari, kuma akwai kudirin da yake gaban majalisar tarayya ta kasa wadda muka sawa hannu a majilisa ta bakwai domin a tabbatar da ’yanci da kuma cin gashin kai na majalisar dokoki na jihohin kasar mu baki daya, don haka za mu sake tado da wannan batu, tunda mun san cewa, mai girma Shugaba Muhammadu Buhari zai amince kuma zaisa hannu a wannan dokar, domin hakan zai kara karfafa dimokuradiyya kana zai tabbatar da yanci na ‘yan majalisa yadda za su tabbatar suna aikin su yadda ya kamata ace ana gudanar da shi da san mai girma Shugaba Muhammadu Buhari zai goyi bayan hakan.