Sanin Ubangiji da kuma kwallafa rai ga al’amuran mulkinSa (2)

Kamar yadda muka yi nazari a makon jiya, za mu ci gaba ne a kan muhimmin abin da ya kamata mu bi a rayuwarmu ta yau da kullum.Matiyu 6:33; Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah da kuma adalcinSa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.Abin lura a […]

Sanin Ubangiji da kuma kwallafa rai ga al’amuran mulkinSa (2)
Sanin Ubangiji da kuma kwallafa rai ga al’amuran mulkinSa (2)

Kamar yadda muka yi nazari a makon jiya, za mu ci gaba ne a kan muhimmin abin da ya kamata mu bi a rayuwarmu ta yau da kullum.
Matiyu 6:33; Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah da kuma adalcinSa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.
Abin lura a nan shi ne kada bukatunmu su zama mafiya muhimmanci fiye da sanin al’amuranUbangiji, domin idan muka sa su gaba da komai cikin rayuwarmu, sukan iya kai mu ga hallaka – fadawa cikin tarkon annabawan karya, muna ta shige-shige daga wannan majami’a zuwa waccan domin neman biyan bukata. Idan muka duba cikin Littafi Mait sarki, Yesu Almasihu ya nuna mana a lokacin da ya koya wa almajiransa yin adud’a a cikin Littafin Matiyu 6:9 -11: “Saboda haka sai ku yi addu’a kamar haka: ‘Ya Ubanmu, Wanda Yake cikin sama, a kiyaye sunanKa da tsarki, mulkinKa ya zo, a aikata nufinKa a duniya kamar yadda ake yi a sama. Ka ba mu abincinmu na yau…” A nan za mu ga cewa bukatunmu (…ka ba mu abincinmu na yau) na biye, neman nufin Allah ya kasance a duniya wato a rayuwarmu ita ce ta farko. Idan har bukatunmu ne muka nema da farko babu shakka idan muka samu biyan bukata, za mu bar yin addu’a za mu nemi nufin kanmu ya kasance, shi ya sa Ubangiji Ya fi so mu nemi saninSa mu kuma kwallafa ranmu ga al’amuranSa da farko.
Sanin Ubangiji ba wani abu ba ne da wani zai gaya maka, ko kuma ya nema wa kansa sa’annan ya ce maka ka zo, shi ya san Ubangiji saboda haka shi (mutum) zai iya biyan bukatunka. Sanin Ubangiji na samuwa ne cikin binciken Littafi Mai tsarki tare da yin addu’a a kodayaushe. Joshuwa 1:8: “Kada wannan littafin dokoki ya rabu da bakinka, amma zai zama abin da za ka yi ta tunani a kansa dare da rana domin ka kiyaye, ka kuma aikata bias gadukan abin da aka rubuta a ciki, gama ta haka za ka yi albarka cikin hanyarka, ta haka kuma za ka yinasara.” To me zai hana mu binciken Littafi Mai tsarki domin sanin Ubangiji da kuma al’amuranSa? Idan ka duba tsawon shekarunka a duniya yau, misali mu ce kana da shekara 20 ko 50, kuma ka koyi karatu a lokacin da kana da shekara 15, za ka iya ba da dalilin rashin binciken Littafi Mai tsarki tun daga wancan lokaci zuwa yau? Me ya sa ba ka iya ka bincika Littafi Mai tsarki ba daga Farawa zuwa WahayinYahaya? Mene ne ya fi muhimmanci a rayuwanka? Harkokin yau da kullum ko al’amuran Ubangiji? Ka yi nazari a kan wannan.
2 Timoti 5:15-19: “Ka himmantu, ka miƙa kanka yardajje ga Allah, ma’aikaci wanda ba hanya ya kunyata, mai kuma fassara maganar gaskiya daidai. Ka yi nesa da masu maganganun banza na sabo. Sai da jan mutane zuwa garashin bin Allah suke yi, 17 maganarsu takan habaka kamar gyambo. A cikin suhar da Himinayas da Filitas, 18 waɗanda suka baude wa gaskiya suna cewa tashin matattu ya riga ya wuce, suna jirkitar da ban-gaskiyar wadansu. 19 Duk da haka, kakkarfat harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa.” Da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunanUbangiji, to, ya yi nesa da aikata mugunta.”Abin tausayi shi ne mutane da dama yau ba su dauki sanin Ubangiji komai ba, sanin kansu da son kansu ya sha gaban komai, ba su ma da lokacin yin addu’a da asuba don gode waAllah cewa suna cikin rayayyu. Za ka ga mutum ya yi asubanci wai shi dan kasuwa, zai je kasuwanci ko ofis ko gona don kada ya makara, har ya manta da lokacin yi wa Allah godiya balle lokacin binciken LittafinSa. Sannan idan wani abu ya faru da su ko kuma ba su yi kasuwa ba, sai su yi ta guje-gujen neman wasu ko majami’u don addu’a? Ka tuba kada ka hallaka a mugun zamanin da muke ciki yau. Masu ja don Ibilis na ko’ina kewaye da mu don su kai marasa bin al’amuran Ubangiji ga hallaka.
Za ka iya fara binciken Littafi Mai tsarki na minti 30 a kowace rana na wata daya wato wajen kwana 30, kana yi tare da addu’a, babu shakka za ka ga abin da Allah zai yi a rayuwarka a kwana-a-tashi za ka ga cewa ka iya karanta Littafi Mai tsarki daga Farawa har zuwa karshe, kuma ba wanda zai iya rinjayarka da wani zance da ba naUbangiji ba. Karanta Littafi Mai tsarki da sanin Ubangiji ba na fastoci ba ne kadai, na kowa da kowa ne, hakan nan yin addu’a. Idan fa muka saUbangiji a gaba, babu shakka komai zai bi hanya a rayuwarmu kuma ba za mu bata ba.
Ubangiji Allah Ya albarkace mu, amin.