Saniya ta haifi ’ya mai kafa biyu

Wani manomi kuma babban mai harkar  sayar da shanu mai suna Wang Shiyouhe ya sayi wata saniya, wanda ta haifi ’ya mai kafafu biyu. Sama da mako daya da sayan saniyar, wani daga cikin abokan Wang ne ya sanar da shi abin da yake faruwa game da haihuwar saniyar da ya saya. Wang mazaunin kauyen […]

Saniya ta haifi ’ya mai kafa biyu

Wani manomi kuma babban mai harkar  sayar da shanu mai suna Wang Shiyouhe ya sayi wata saniya, wanda ta haifi ’ya mai kafafu biyu. Sama da mako daya da sayan saniyar, wani daga cikin abokan Wang ne ya sanar da shi abin da yake faruwa game da haihuwar saniyar da ya saya.

Wang mazaunin kauyen Henan a Lardin Shandong da ke Gabashin China, ya ce bai taba ganin haihuwar dabba irin wannan ba musamman saniya duk da shekarun da ya kwashe yana kasuwancin dabbobi.

Wang ya yanke shawarar sayar wa kansa ’yar saniyar saboda yanayin halittarta, kuma yana kashe wa ’yar saniyar Naira dubu 2 da 841 da kwabo 26 kullum wajen sayen madara, kuma yana da shirin kiwon ’yar saniyar duk da yanayin halittar da take da shi.

Duk da yake ’yar saniyar tana da halitta irin ta dabbar daji da ake kira Kangaroo sakamakon yadda take da kafafu biyu, Wang ya ce, kasancewar ba ta iya tafiya zai koya mata yadda za ta yi tafiya.

Wang ya kara da cewa, “Kamar yadda take da cikakkiyar lafiya, zan ci gaba da kiwonta har zuwa karshen rayuwarta.”

Halittar ’yar saniyar ta kasance abin kallo, musamman jama’ar garin sukan ziyarci inda take don ganewa idonsu abin al’ajabi da saniya ta haifa.

’Ya’yan Wang, sun kasance suna shayar da ’yar saniyar madara da robar shayar da jarirai.

 

Ambaliya: Binani ta bai wa Maiduguri tallafin 50m

An sallami sojar da ta zargi shugabanta da neman lalata da ita

CBN ya ƙara kason kuɗin ruwa zuwa 27.25 cikin 100

Hatsarin kwalekwale ya ci rayuka 4 a Borno