Saniya ta kai wa marasa lafiya farmaki a asibiti
Jaridar Banguardia ta ce, mai saniyar ya je asibitin don ba marasa lafiyar da saniyar ta razana hakuri, ciki har da matar da saniyar ta raunata.
Wata saniya da ta kwace daga turkenta ta auka cikin wani asibiti inda ta kai wa marasa lafiya farmaki tare da wargaza kujeru.
Lamarin dai wanda ya faru a kasar Kwalombiya ya kuma jefa firgici da tsoro a zukatan mutanen asibitin.
- ‘Babu mahalukin da ya isa ya karya Gwamnatin Buhari’
- Sam Buhari bai fahimci zanen gadar da Ganduje ya kai masa ba – Kwankwaso
Na’urar daukar hoton bidiyo ta CCTV ta nuna yadda saniyar ta fara kutsa kai cikin dakin baki na asibitin sannan ta fara yawo a cikin asibitin.
Ko a farkon wata Fabrairun bana dai sai wani Sa ya taba shiga cikin wani shagon ’yan China a ranar 13 ga watan Fabrairun bana.
Bayan shigar saniyar asibitin ne dai wasu mutane suka fara neman mafaka amma ta ci gaba da bin su har sai da ta kai sun rufe kofofi da tagoginsu.
Hoton bidiyon ya nuna yadda saniyar ta rika tafiya tana faduwa, lamarin da ya tilastawa marasa lafiya tserewa, amma an bar wadansu mata kwance a kasa bayan samun raunuka, yayin da wadansu maza biyu suka yi kokarin fitar da saniyar daga cikin asibitin.
Lamarin dai ya faru ne a asibitin San Rafael a tsangayar Antiokuia da ke birnin St. Luis na kasar ta Kwalombiya.
Bidiyo na biyu ya nuna yadda lamarin ya faru daga wajen harabar asibitin inda wasu mutane suka fara ihu da hura usir yayin da wadansu suka yi ta tserewa.
Jaridar Banguardia ta birnin ta rawaito cewa babu ko mutum daya da ya samu mummunan rauni yayin farmakin saniyar a asibitin, sai dai mata daya da ta rikice tare da jin ciwo, yayin da sauran ba su bukaci wani magani daga asibitin ba.
Saniyar dai ta lalata babura biyu a kofar shiga asibitin tare da wasu kujeru.
Jaridar Banguardia ta ce, mai saniyar ya je asibitin don ba marasa lafiyar da saniyar ta razana hakuri, ciki har da matar da saniyar ta raunata.
Sai dai rahoton bai bayyana ko mai saniyar zai biya asarar da saniyar ta jawo wa asibitin ko a’a ba.