Saniyar da ta fi kankanta a duniya ta mutu
Wata saniya da aka tabbatar ta fi kankanta a duniya ta mutu bayan da ta shahara a farkon bana saboda kankantarta. Saniyar mai shekara biyu mai suna Rani, gajera ce mai tsawon sentimita 51 (inci 20) kuma tana da nauyin kilo 28 (laba 62l), hakan ya sa manajan gonar da aka haifi saniyar yake alfahari […]
Wata saniya da aka tabbatar ta fi kankanta a duniya ta mutu bayan da ta shahara a farkon bana saboda kankantarta.
Saniyar mai shekara biyu mai suna Rani, gajera ce mai tsawon sentimita 51 (inci 20) kuma tana da nauyin kilo 28 (laba 62l), hakan ya sa manajan gonar da aka haifi saniyar yake alfahari da samun saniyar da ta fi kowace saniya kankanta a duniya.
Saniyar wadda aka yi kiwonta a wani gari da ke kusa da Dhaka babban birnin kasar Bangladesh ta mutu ne saboda “yawan cin abinci” da “tarin iskar gas a cikinta,” inji wani rahoto da jaridar The Mirror ta ruwaito.
An garzaya da Rani wajen likita don neman agajin gaggawa a makon jiya, lokacin da aka lura cewa cikinta ya kumbura, amma likitocin dabbobi ba su iya yin komai don ceton rayuwarta ba. Hakan ya yi sanadin mutuwarta, “cikin awanni.”
Saniyar ta shahara a manyan kafafen yada labarai a watan Yuli lokacin da manajan gonar da take mai suna Hasan Howlader ya aika da sakamakon awon saniyar zuwa Kundin Littafin Tarihi na Duniya (Guinness Book of World Records) don fatar ganin saniyar ta dauki kambin saniyar da tafi gajarta a duniya.
An ba da rahoton cewa, sama da mutum dubu 15, sun ziyarci saniyar a gonar da ake kiwonta a Charigram, kusa da birnin Dhaka.
Kundin tarihi na Guinness World Record ya wallafa cewa saniya mafi gajarta a duniya a halin yanzu ita ce Manikyam a Jihar Kerala da ke kasar Indiya, da take da tsawon santimita 61.1 (inci 24).
Jami’ai daga gidauniyar Guinness sun ziyarci Manikyam kuma sun yi magana da likitan dabbobi Dokta E M Muhammed, wanda ya yi bayani kamar haka:
“Kimanin shekara biyu da suka gabata, mun fahimci cewa wannan dabbar ta fi gajarta a kowane jinsin shanu. Manikyam tana da kimanin shekara hudu a lokacin, amma tun tana da wata 9 ko 10 muka fahimci cewa, akwai wani abu daban game da ita. Mun aunata sosai tun tana shekara biyu. Lokacin da take da shekara hudu, tana da da tsawon santimita 64 (kafa 2 da inci 1).”
Yawancin shanunmu na gida suna da tsawon santimita 150 (kafa 4 da inci 11) . Manikyam jinsin shanun Vechur ne, sanannu ne wajen samar da shanu masu gajarta. Jinsin Vechurs sukan yi girma zuwa matsakaicin tsawo kusan santimita 90 ne.