Saniyar Tatsa
Tun da Gwamnatin Muhamadu Buhari ta fara kakkabo ha’incin da azzaluman shugabanni da manyan jami’an gwamnati na soji da farar hula suka tattafka a lokutan baya, sai ‘yan Najeriya suka mayar da lissafin biliyan da tiriliyan tamkar Naira dari ko dubu ne kadai, domin kuwa ba su jin ana cewa, wasu manyan kasar nan na […]
Tun da Gwamnatin Muhamadu Buhari ta fara kakkabo ha’incin da azzaluman shugabanni da manyan jami’an gwamnati na soji da farar hula suka tattafka a lokutan baya, sai ‘yan Najeriya suka mayar da lissafin biliyan da tiriliyan tamkar Naira dari ko dubu ne kadai, domin kuwa ba su jin ana cewa, wasu manyan kasar nan na sace dubban daruruwan Nairori ko wasu ‘yan miliyoyi, sai adadin da hankali ba zai iya amincewa da cewa barawo na iya awon gaba da su a tashi guda ba. A lokacin ne talakawa suka fahimci cewa satar da aka yi musu ta keta ce, kuma ba ‘yar kadan ce ba, kuma sata ce ta rashin imani, domin barayin sun jidi abin da ba za su iya kashewa ba iyakar tsawon rayuwarsu, kuma wasu ko da a kullum za su kashe miliyan guda ne sai sun yi shekaru 50 ba su batar da rabin abin da suka sata ba. To a nan sai a ce ina ranar sata irin waccan ke nan?
Idan aka dubi wani rahoton kwanannan da babban mai binciken kudin gwamnatin tarayya, watau Auditor-General sai a fahimci cewa hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya dai sun kasance ramin gafiyoyin da ke dibga satar da ta sa Najeriya ta yi kaurin suna dangane da haka a kasashen duniya. Alal misali, a cikin rahoton binciken kudaden da aka sarrafa a shekarar 2014, wanda aka gabatar wa majalisun kasa a kwanakin baya, Babban Mai binciken Kudin Samuel Ukura, ya fayyace wata kissa mai ban takaici da ban tsoro game da wasu aikace-aikacen almundahana da aka tattafka wajen salwantar wasu kudin da suka kai miliyan dubu-gida-dubu barkatai a hukumomin mai ta NNPC da kuma ofishin Mai Bayar da shawara ga shugaban kasa game da harkokin tsaro da kuma hukumar ‘yan sanda. Daga cikin abin da ya fi tayar da hankula game da cuwa-cuwar da aka yi, shi ne, yadda aka yi rub-da -ciki bisa wasu kudin da suka shiga hannun Hukumar NNPC, amma ta ki tsibe su a baitul-malin gwamnati, har Naira miliyan dubu-gida-dubu-uku da dari biyu, duk kuwa da cewa sauran abubuwan da aka bankado a wasu hukumomin su ma suna tayar da hankali ainun.
Akwai kuma wasu Dalar Amurka miliyan 235, wadanda hukumar Gas ta Najeriya ta aike da su wata ajiyar banki ta wucin gadi a kasashen waje, maimakon a ajiyar gwamnatin tarayyar Najeriya da ke can kasar waje sakamakon iskar gas din da aka sayar a can. Akwai kuma kissar wasu Naira miliyan dubu 36 da 400 na wata madatsar ruwa da aka fitar don ginawa, amma sai aka tsiyaya kudin a ajiyar Mai Bayar da Shawara Ga Shugaban kasa a harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki Mai ritaya, maimakon Ma’aikatar Albarkatun Ruwa. Akwai kuma hikayar wasu Naira miliyan dubu biyu da dari tara da aka ambato cikin rahoton binciken da aka ce an fitar da su ne domin sayen kayayyakin wanke hannuwan yara a makarantu da kuma wasu muhimman wuraren da jama’a ke taruwa; sai kuma bayanin wasu Naira miliyan dubu talatin da daya da dubu bari uku da aka fitar don bayar da tallafi ga farashin takin zamani da taimaka wa matasan da ba su da aikin yi don shiga aikin gona; akwai kuma batun wasu Naira miliyan dubu biyar da dari biyu da aka cire kai tsaye a matsayin kashi daya bisa dari na kason gwamnatin tarayya na wasu kudin kyautata wa ‘yan sanda; ga kuma bayanin wasu Naira miliyan dubu biyu da dari hudu da aka wafce a matsayin yi wa sojoji inshora; sai kuma asirin da ya tonu game da wasu Naira miliyan dubu dari da tamanin da ba a nuna su ba alhali kuwa an karbe su da sunan kudin rarar farashin man fetur don ayyukan dakushe kaifin fatara da ake kira SURE-P; sa’annan kuma an gano cewa an fitar da wasu Naira miliyan dari takwas da uku daga Ma’aikatar Raya Yankin Neja Delta. Kai ka ji abu sai ka ce almara da littafin Alfu-laila-wa-lailatun.
Wadannan batutuwa masu tayar da hankali ne kwarai da gaske, domin kuwa an dade ana tafka ta’asa irin haka ba tare da an dauki matakan hanawa ko hukunta masu aikatawa ba. Bincike na da fa’ida domin yakan taimaka wa gwamnati fahimtar halin da ake ciki don ta tabbatar an aikata zamba da magudi da dukiyar jama’a, sa’annan kuma talakawa su gane yadda ake cutar su. Duk da cewa an yi jinkiri wajen yin bincike irin haka, amma ai da babu gara ba dadi. Yanzu dai Babban Mai Binciken Kudin Gwamnati ya yi aikin da dokar kasa ta bukace shi da yi, ya kuma rage wa kwamitin Kula da Kudin Al’ummna, na Majalisun kasa, watau Public Accounts Committees su ci gaba daga inda Babban Mai Binciken KudI ya tsaya, ya kuma nemi karin haske kan wasu al’amuran da aka bankado da niyyar gano dabarun da aka bi don kauce wa ka’idojin da aka gindaya wajen mu’amala da kudin jama’a, da kuma yadda aka yi awon gaba da kudin, har aka sake musu ma’ajiyar da ba ta kamata ba. To da zarar an yi haka, sai kuma a iza keyar azzaluman da aka tabbatar sun aikata ta’asa dangane da binciken gaban alkalan da za su hukunta su.
To amma idan aka duba sai a fahimci cewa, babu ta yadda za a yi a caba wadancan almundahanar da aka gano ba tare da sakaci ko hadin bakin ‘yan majalisun kasar nan ba da aka dora wa hakkin binciken yadda jami’an hukumomi da ma’aikatun gwamnati ke batar da kudin da aka danka musu amana, domin kuwa idan da suna sanya idanu yadda ya kamaya kan amanar dukiyar da aka ba jami’an gwamnati, su kuma tsawata idan sun ga za a yi sama da fabI da su, ai da haka bai faru ba. To amma su ma sun kallafa ransu kan wadancan dukiyoyin da ake sassacewa, ana kuma ba su nasu kason idan har an wawuro, ko kuma akan haba baki da su a yi aringizon kudi a wani aji yayin tsara kasafin kudi, alabarshi daga bisani a yi musu kashi mai dumi da abin da aka dora cikin kasafin. Muddin dai ba jami’an gwamnati sun daina tunanin cewa kudin da ake ba su ba na uban kowa ne ba, suna iya tumurmusa, su kwana lafiya, jami’an hukumomin da ya kamata su tsawata kuma suna sanya musu ido don a fitar musu da nasu, to ba ta yadda za a yi a yi bankwana da gadara da izgilanci wajen satar rashin kunya a wannan kasar da ta rigaya ta yi kaurin suna wajen samar da shugabanni masu kuruciyar bera da suka mayar da Najeriya saniyar tatsa.