Sanjay Dutt ya yi bikin haihuwarsa a kurkuku

A Talatar da ta gabata ce dan fim din Indiya, Sanjay Dutt ya cika shekara 54 da haihuwa. A wannan karon, jarumin ya yi bikin haihuwar tasa ne a gidan jarun.Duk da cewa yana daure a gidan maza, abokansa na kut-da-kut ba su bari ya ji kunya ba, domin kuwa sun aika masa da wasiku […]

Sanjay Dutt ya yi bikin haihuwarsa a kurkuku

Dan fim, Sanjay DuttA Talatar da ta gabata ce dan fim din Indiya, Sanjay Dutt ya cika shekara 54 da haihuwa. A wannan karon, jarumin ya yi bikin haihuwar tasa ne a gidan jarun.
Duk da cewa yana daure a gidan maza, abokansa na kut-da-kut ba su bari ya ji kunya ba, domin kuwa sun aika masa da wasiku na musamman, suna taya shi murna. Wadanda suka aika da wasikun sun hada da Ranbir Kapoor da Rajkumar Hirani da kuma Bunty Walia.
Kamar yadda mujallar Zee News ta ruwaito, dan wasan yana rufe ne a gidan yarin Pune Yerawada, abokan nasa sun aika masa da wasikun ne da nufin faranta masa rai, a yayin da yake daure.
“Mu abokan sana’arsa, mun bukaci mu taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Muna son mu sanar da shi cewa muna tunawa da shi kuma muna kewarsa. Ta hanyar wasika ce kawai za mu gana da shi kuma mu gaishe shi.” Inji daya daga cikin abokan nasa da suka aika masa wasika.
Wata majiya kuma ta sanar da mujallar cewa, iyalansa ne kawai aka amince su gana da shi sau daya a wata, kuma ga shi sai cikin Agusta ne wannan ganawa za ta zo, don haka suka zabi su aika masa wasiku, domin ya samu farin ciki a ranar haihuwarsa.