Cutar sankarau ta kashe mutum 118 a jihohi 22 na Najeriya —NCDC

Kashi 93 cikin 100 na dukkan wadanda suka kamu da cutar sun fito ne daga jihohi biyar.

Cutar sankarau ta kashe mutum 118 a jihohi 22 na Najeriya —NCDC

Cutar sankarau ta kashe akalla mutane 118 a jihohi 22 na wasu kananan hukumomi 79 a Najeriya.

Alkalumma sun bayyana cewa kawo yanzu an samu mutane 235 da aka tabbatar sun kamu da cutar sannan ana zargin mutum 1,479 sun kamu da cutar.

Ya zuwa yanzu dai alkalumma sun tabbatar an samu kashi 9.3 cikin dari da suka mutum cikin wadanda suka harbu da cutar.

Alkaluman dai na zuwa ne bayan an samu karin mutane 23 da suka mutu sakamakon harbuwa da cutar ta sankarau, tare da 212 da aka tabbatar sun harbu da cutar a cikin jihohi 3 na kasar.

A wani sabon rahoto da ta fitar a jiya Asabar, Cibiyar Yaki da Cututtuka NCDC ta ce adadin wadanda suke harbuwa da cutar a duk mako a lokacin da ta yi bincikenta daga 27 ga watan Maris zuwa 2 ga Afrilu sun kai kaso 8.

Rahoton na cibiyar ya nuna cewa Jihar Jigawa a Arewa maso Yammacin kasar ce ke da kaso 62 na wadanda suka harbu da wannan cuta.

A jihohin Yobe da Adamawa da ke Arewa maso Gabashin kasar, an samu mutane 4 da suka harbu da cutar a kowannensu na da kaso 17.

Cibiyar ta ce daga cikin mutane 23 da suka mutu sakamakon cutar, 17 daga Yobe ne, a yayin da 9 suka mutu a Jigawa.

Kashi 93 cikin 100 na dukkan wadanda suka kamu da cutar sun fito ne daga jihohi biyar – Jigawa (1,064), Yobe (234), Zamfara (36), Bauchi (23), da Adamawa (21).

Rahoton ya kara da cewa, “Kananan hukumomi goma sha hudu da abin ya shafa a fadin jihohi hudu sun hada da Jigawa (8), Yobe (4), Bauchi (1) da Zamfara (1).

Jihohin 22 da aka samu rahoton bullar cutar sun hada da Abiya, Adamawa, Bauchi, Bayelsa, Benuwe, Borno, Ebonyi, Gombe, Imo, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Nasarawa, Neja, Oyo, Filato, Sakkwato, Taraba, Yobe da Zamfara.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Tags