Sankarau ta kashe mutum 56 a Najeriya —NCDC
Hukumar NCDC ta ce 961 sun kamu da cutar sankarau a fadin Najeriya
Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta ce ana zargin mutum 56 sun mutu sakamakon cutar a sankarau a Jihohi 32 da Birnin Tarayya, Abuja.
A ranar Laraba NCDC ta sanar ta hannun Babban daraktanta, Dokta Ifedayo Adetifa, cewa mutum 961 sun kamu da cutar.
Sanarwar ta ce, duk da kokarin da kasashe ke yi wajen yaki da wannan cuta, amma har yau tana daga cikin cututtukan da ke yi wa lafiyar al’umma barazana.
Sankarau cuta ce da akan samu bullarta duk shekara a Najeriya, musamman a jihohin Arewa.
NDCD ta ce Najeriya ta shiga sahun kasashen duniya masu kudirin ganin bayan wannan cuta ya zuwa 2030.
Ranar 5 ga Oktoba na kowace shekara, ita ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don wayar da kan al’umma dangane da cutar a fadin duniya.