…Sankarau ya hallaka mutum 36 a Kebbi
Kimanin mutum 480 ne suka kamu da cutar sankarau a Jihar Kebbi, inda mutum 36 daga cikinsu suka riga mu gidan gaskiya. Wani babban jami’i a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kebbi Alhaji Sani Yusuf Argungu ne ya bayyana wa wakilinmu haka a ofishinsa da ke sakateriyar gwamnatin jihar a Birnin Kebbi.Babban jami’in ya ce cutar […]
Kimanin mutum 480 ne suka kamu da cutar sankarau a Jihar Kebbi, inda mutum 36 daga cikinsu suka riga mu gidan gaskiya.
Wani babban jami’i a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kebbi Alhaji Sani Yusuf Argungu ne ya bayyana wa wakilinmu haka a ofishinsa da ke sakateriyar gwamnatin jihar a Birnin Kebbi.
Babban jami’in ya ce cutar ta bulla ne a kananan hukumomi shida daga cikin kananan hukumomi 21 da ke jihar, kuma kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Gwandu da Argungu da Jega da Aliero da Zuru da Birnin Kebbi.
Alhaji Sani Argungu ya ce a bana cutar ta canja salo daga yadda aka santa, maimakon wadda aka fi sani mai rukunin A, yanzu cutar ta fito da rukunnin C, inda ya ce ba a riga an yi tanadin maganinta ba.
Ya ce duk da haka gwamnatin jihar ta taka rawar gani tare da hadin kungiyar likitoci masu sa-kai da suka kawo magungunan rigakafi domin ba wadanda suka kamu da cutar.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa ban da wadannan kananan hukumomi da babban jami’in ya zayyana an samu barkewar cutar a wasu kananan hukumomin na daban.
Alhaji dahiru Nayaya Ambursa shi ne kantoman yankin raya kasa na Kardi-Ambursa ya tabbatar wa Aminiya bullar cutar a wani gari mai suna Unguwar Kware da yankinsa, inda ya ce har mutum hudu sun rasa rayukansu a sanadiyyar cutar.