Sansanin ’yan gudun hijira

Abubuwa da dama kuma munana ke sabbaba yin gudun hijira daga wani wuri zuwa wani don samun sa’ida.Kuma kowa ya san gudun hijira ba abu ne mai dadi ba, don haka babu wani mahaluki a doron kasa da zai yi sha’awar tsintar kansa  a cikin wannan hali domin kuwa ba a sanin wane irin hali […]

Sansanin ’yan gudun hijira
Sansanin ’yan gudun hijira

Abubuwa da dama kuma munana ke sabbaba yin gudun hijira daga wani wuri zuwa wani don samun sa’ida.Kuma kowa ya san gudun hijira ba abu ne mai dadi ba, don haka babu wani mahaluki a doron kasa da zai yi sha’awar tsintar kansa  a cikin wannan hali domin kuwa ba a sanin wane irin hali za a tsinci kai a ciki ba yayin da aka yi wannan hijira.

Wadansu na yin hijira ne a dalilin wata annoba da ta barke a wurin da suke zaune, wadansu na yi ne saboda takurar da suke samu daga jama’ar wurin, wadansu kuwa na yi ne saboda rashin samun sukunin aiwatar da wani abu da suke son yi, wadansu kuma tsangwama ke sa su yin hijira. Mu kuwa a nan Najeriya musamman Arewa (ko in ce Arewa maso Gabas) ana ambatar kalmar gudun hijira, ba abin da ke zuwa ran kowa sai ta’addancin Boko Haram, domin kuwa kafin wannan matsala ta Boko Haram ba mu san mece ce gudun hijira ba, sai dai kawai mu ji ta a labarai. Amma daga bayyanar wannan matsala kawo yanzu babu wani mutum ko wata hukuma ko wata kungiya da za ta iya bayyana adadin mutanen da suka yi gudun hijira suka bar muhallansu a yankin, sai dai kawai a yi kintacen haka sannan ba a san adadin rayukan da suka salwanta ba balle a san adadin dukiyar da aka rasa.

Hakika gwamnati ta yi kokari wajen samar da sansanonin ’yan gudun hijirar a ciki da kuma makwabtan jihohin da matsalar tafi shafa, kuma gwamnati da kungiyoyin sa-kai na ciki da wajen kasar nan suna kokari wajen samar wa ’yan gudun hijirar magunguna don kiwon lafiyarsu. Tabbas! Ni ganau ne ba jiyau ba, domin na ziyarci daya daga cikin sansanonin ’yan gudun hijirar a lokacin da na kai wata ziyara Jihar Borno. Na je daya daga cikin sansanonin da suke da shi wanda yake hanyar zagaye (Bye Pass) a Maiduguri.

Gaskiya sansanin babba ne ga gine-gine masu kyau a ciki ga ruwan sha mai tsabta, a gefe guda kuma ga jami’an tsaro na soji da ’yan sandan kwantar da tarzoma a mashiga da kuma gefe da gefe. Sannan na hadu da jami’an Kungiyar UNICEF sun zo duba ma’aikatansu can gefe kuma sai na hangi tarin mutane sun hau layi yara da manya mata da maza. Sai na tambayi wata ma’aikaciyar lafiya ta Hukumar UNICEF wacce ta sanadiyyarta ce na je wannan wuri cewa me ke faruwa? Ta fada min cewa kayan abinci ne ake raba musu, abin a yaba domin kuwa kayan abinci ne masu kyau da tsada wadanda ba kowa daga cikinsu ne zai iya saya ba. Haka wadansu daga cikinsu sukan fita su yi sana’a wadansu ma a ciki suke yin sana’ar tasu.

Sai dai kuma duk wannan kula da suke samu ana yin tuya ce babu albasa domin kuwa an manta da babban jigon rayuwa a wannan sansani kuma jigon abin da ke haddasa kusan duk wani ta’addanci wato rashin ilimi, domin kuwa tunda na shiga wurin da misalin karfe 11 na safe har zuwa lokacin da na taho da yamma ban ga wurin samar da ilimi (makaranta) ba, walau ta addini ko ta zamani ban kuma ji an ambaci cewa akwai makaranta a wurin ba, wanda kuma ina ganin hakan kamar zai iya mai da hannun agogo baya wajen ganin sun samu rayuwa mai kyau. Don haka ya kamata gwamnati da kungiyoyi da masu hannu da shuni su taimaka wajen samar da makarantu a dukkan sansanonin ’yan gudun hijirar.

Akwai abubuwan da idan mutum ya gani dole ya ji ba dadi a ransa kamar irin fasadin da ake aikatawa a ciki domin kuwa da yawa daga cikinsu sun mai da zina kamar ado. An nuna min yaran da aka same su ta mummunar hanya an kuma nuna min masu juna biyu da suka samu a kan layi. akwai kuma yara sababbin haihuwa da ake tsinta akwai ma wacce aka ce ta haihu a dakin shan maganin da ke wurin, da ungozomar da ke kula da ita ta fita don samo wani abu kafin ta dawo yarinyar ta tashi daga gadon da take ta gudu ta bar jaririn. Wannan abin kaico ne! Yana da kyau gwamnati ta samar musu da makarantu kuma a canja fasalin zamantakewarsu sakamakon suna kwana ne mata da maza a cikin daki guda. Kowane sansani haka yake fama da wadannan matsaloli don haka muna kira ga gwamnati ta kara taimakawa ta hanyar ba su ilimi. Ilimi dai kowa ya sani shi ne hasken rayuwa, don haka idan ba ilimi ana iya fadawa cikin kowane irin yanayi marar kyau.

Kuma wannan shi ne karshen gata ko taimako da za a yi wa kowane mutum ba iya ’yan gudun hijira ba wato a ba shi ilimin addini da na zamantakewa ko boko. Allah Ya kawo mana karshen tashe-tashen hankulan da ake fama da su a Arewa da Najeriya baki daya.

  1. Bello Kiyawa (070-3252-8895) [email protected]