Sansantawa tsakanin Adam Zango da dan jarida: Da sauran rina a kaba

A yanzu dai batun sasantawa tsakanin fitaccen jarumi Adam A. Zango da kuma Editan Mujallar Fim akwai sauran rina a kaba. Mun kawo muku labarin yadda Editan Mujallar Fim Aliyu Gora II ya kai karar jarumi Adam A. Zango ofishin ‘yan sanda na Metro da ke Kaduna, inda ya ce ya lakada masa duka har […]

Sansantawa tsakanin Adam Zango da dan jarida: Da sauran rina a kaba

A yanzu dai batun sasantawa tsakanin fitaccen jarumi Adam A. Zango da kuma Editan Mujallar Fim akwai sauran rina a kaba.
Mun kawo muku labarin yadda Editan Mujallar Fim Aliyu Gora II ya kai karar jarumi Adam A. Zango ofishin ‘yan sanda na Metro da ke Kaduna, inda ya ce ya lakada masa duka har ya yi masa karo, zargin da jarumin ya karyata.
‘Yan sanda sun ci gaba da bincike wanda ta sanya a makon da ya gabata muka bayyana muku har lokacin da muka hada rahoton ba a kai ga cimma matsaya ko a tafi kotu ko kuma a sasanta ba.
bangarori biyun sun koma ofishin ‘yan sandan a ranar Alhamis din makon jiya, inda kuma aka yi nasarar sasanta su bisa sharadin Mujallar Fim za ta daina buga labarin batanci kamar yadda su Zango suka zarge su da yi, inda kuma su ma su Zango suka rubuta takardar ba da hakuri hade da alkawarin ba za su sake maimaita irin hakan ba. A takaice dai aka wanzar da harsashin zaman lafiya.
Editan ya ce: “Mun koma ofishin ‘yan sanda, a karshe an sasanta mu sakamakon shigowa da wasu da Adamu ya yi, amma ya rubuta takardar ba da hakuri da kuma alkawarin ba zai sake maimaita irin hakan ba.”
bangaren jarumin sun shaida wa wakilinmu batun sasantawar, sun kuma karbeta da zuciya daya, sai dai bayan Mujallar Fim ta wannan watan (Agusta) ta fito ne sai aka ganta da labari mai taken: ‘Zango ya zare, ya fara bugun mutane’. Al’amarin da ya dawo da tsohon ciwo sabo, dangantaka ta kara tsami tsakanin bangarorin.
Wata majiya ta kut-da-kut da jarumin ta yi wa Aminiya bayani kamar haka: “Mun koma ofishin ‘yan sanda a ranar Alhamis din makon jiya, inda Mujallar Fim suka amince za su daina rubuta labarin batanci a kan Zango. A nan kuma muka yi yarjejeniyar zaman lafiya da su, amma abin mamaki sai muka ga labarin ‘Zango ya zare, ya fara bugun mutane’ a cikin mujallarsu ta wannan watan. Abin ya ba mu mamaki, muka ce ga abin da suka saka mana da shi tun yanzu.”
“Daga nan na tura wa Gora sako, shi ma Zango ya tura masa sako, masoyanmu da yawa sun kira mu sun ce sun tura masa sako. A sakonnin mun ce: mun yi yarjejeniyar zaman lafiya, amma kuma ga abin da kuka rubuta. Sai dai Gora bai turo mini sako ba, bai kuma tura wa Adamu ba. Amma ya samu wadansu daga cikin shugabannin ‘ yan fim na Kaduna ya ce jikinsa ya mutu. Kuma abin da ake yi masa ba a yi masa adalci. Ya ce yadda kowa ya ga labarin a kasuwa haka shi ma ya gan shi, domin yakan rubuta labari ya tura wa maigidansa Ibrahim Sheme ta imel, wanda kuma shi ke da wuka da nama wurin gyara labarin, a karshe dai sai mujallar ta fito sai ya gan ta a kasuwa. Ya fada wa shugabannin fim na Kaduna da suka hada da A. A. Rasheed da Rilwan  Smart da A.S Muhmmad da cewa ya sha rubuta labari ya kai wa maigidansa Sheme shi kuma ya tace abin da zai tace har a bugo mujalla. Wai sai jarida ta fito sai ya ga abin da bai san da shi ba.” Inji majiyar.
Ya ce: A takaice dai Gora ya turo su A. A. Rasheed jiya (Talatar da ta gabata), inda suka same mu a gida. Wadanda muka yi zaman sun hada da Abu Sarki da Falalu dorayi da Shehu Jaha da Adam A. Zango da mutane ukun da ya turo. A karshe mun yafe masa saboda azumin watan Ramadana. Kodayake ko a lokacin da muka yi zaman sun ce mana Gora ya ce ko a wannan lokacin ma yana kan tebur yana rubuta takardar barin aiki. Shugabannin fim na Kaduna sun ce za a yi babban zaman sulhu a ranar Lahadi 18 ga watan Agusta, 2013, inda za a yi zaman da Ibrahim Sheme, kuma a nan kowane bangare zai amince idan ya saba shugabanni ko hukuma ta yi masa horo.”
Wakilinmu ya kira editan don ya yi karin bayani dangane da abin da bangaren su Zango suka ce sai ya ce, wannan shifcin gizo ne. Ya ce: “Wannan maganar banza ce, ni ban tattauna da su A. A Rasheed ba, ban kuma san an yi haka ba, a wurinka na fara ji. Babu batun zan ajiye aiki, kuma batun tura wa Sheme labari ta Imel ba haka ba ne.  Suna so su yi amfani da kowace irin kafa ce don bata mini suna.”
Yanzu dai za a iya cewa batun sasantawar tsakanin jarumin da editan har yanzu akwai sauran rina a kaba.