Sanusi Lamido Sanusi a kan yunkurin kasar Sin na karya Masana’antun Afirka

Daga Abdullahi Ahmed Babayaro Masana’antu suna da rawar da suke takawa wajen ci gaban kasashe a duniya gaba daya. Tarihi ya nuna cewa duk kasashen duniya da suka ci gaba irin su Amurka da Faransa da Jamus da Rasha da kuma Ingila duk sun samu habakar arziki ne ta bunkasar masana’antunsu tun fil-azal.Yawan manya-manyan masana’antu […]

Sanusi Lamido Sanusi a kan yunkurin kasar Sin na karya Masana’antun Afirka
Sanusi Lamido Sanusi a kan yunkurin kasar Sin na karya Masana’antun Afirka

Daga Abdullahi Ahmed Babayaro

Masana’antu suna da rawar da suke takawa wajen ci gaban kasashe a duniya gaba daya. Tarihi ya nuna cewa duk kasashen duniya da suka ci gaba irin su Amurka da Faransa da Jamus da Rasha da kuma Ingila duk sun samu habakar arziki ne ta bunkasar masana’antunsu tun fil-azal.
Yawan manya-manyan masana’antu sun zama wadansu muhimmin alamu da ke bayyana karfin kasashe, a yadda kuma suka zama abubuwa masu muhimmanci saboda matsayinsu na hanyar bunkasa tattalin arzikin kasa wajen kasuwanci tsakanin kasa da kasa.
Masanana’antu suna samar da abubuwa da dama a kasa kamar haka: Kudin shiga da matsayin rayuwa da dorewar arziki da daidaituwar kasuwanci da kawo ci gaba a wadansu fannonin da ke kawo arzikin kasa da bunkasa samun aikin yi da yaki da fatara da kawo kwarewa wajen ma’aikata da kasa gaba daya da ci gaba wajen amfani da kayayyaki da hanyoyi na zamani da karuwar kudin ajiya a wajen ma’aikata da budewar kasuwanni daban-daban a kasa da bunkasar samun kudin haraji ga gwamnati don a yi wa al’umma aiki.
Ingila wadda ta mulke mu ce ta fara shigo mana da masana’antu a shekarar 1945 duk da dai cewa sun same mu da masana’antunmu na gargajiya irin su majemar fata da da marina ta rinin kaya da dai sauransu.
Sun kafa wadannan masana’antun ne don matakin farko na sarrarafa kayayyaki irin su fata da auduga da gyada da koko kuma roba da sauransu don kai wa kasar Ingila.
A wannan lokacin an rungumi harkar masana’antu sosai wanda ya sa tattalin arzikin Najeriya ya yi matukar bunkasa, ta hanyoyin samar da kasuwanci da ayyukan yi ga miliyoyin al’umma. kasar gaba daya ta dauwama ne a kan wadannan masana’antu wajen sarrafa wadannan kayayyaki da fitar da su.
A hankali a hankali saboda karancin wutar lantarki, kayan gyaran injina da kayayyakin aiki wannan sashe na masana’antunmu ya fara tangal-tangal amma dai suna kera abubuwa duk da dai dole suka rage yawan kayan da suke kammalawa a kullum.
An samu tabarbarewar al’amura a wannan sashe ne saboda rashin kishin kai da zalunci da magudi da cin hanci da suka yi mana katutu a rayuwar mu ta yau da kullum.
A hankali Sin suka shigo da kayayyakinsu inda suka karya farashin kayansu wanda hakan ya sanya a koma wasoson kayayyakinsu namu kuma suka karye.
Wannan ta sa Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi ya yi wani jawabi a Hong Kong inda ya ankarar da kasashen Afrika cewa mulkin mallakar kasar Sin kan masana’antunmu ba za ta sabu ba bindiga a ruwa, wajibi ne mu fahimci cewa kassara mu suke son yi.
Kowa ya san kishin Lamido Sanusi da jajircewarsa wajen yi wa kasa hidima kuma mutum ne da ba ya tsoron ya fadi gaskiya a ko ina ko da wane ne maganar ta shafa in dai kan ci gaban kasar nan ne.
Ya duba wannan matsalar aringizo da kaya da Sin take ta yi cikin Najeriya sosai kuma ya ga cewa akwai zalunci a ciki.
Abin da ya sa ke nan ya ce Sin ita ce umul’abaisin ci baya kasar nan da ma sauran kasashen Afrika su ke fama da shi ta wajen durkushewar masana’antu da kamfanoni wadanda kan jawo tabarbarewar arzikin kasashe.
Malam Sanusi ya yi wannan magana ne a cikin wata mukala da ya rubuta a shahararriyar mujallar nan da ke New York a Amurka mai suna Financial Times.
Ya yi gargadi da cewa yadda ake rububin kayayyakin Sin kamar ana bude kofar wani sabon mulkin kama karya ne a Afrika, tunda yanzu duk kasuwanninmu da ’yan kasuwarmu sun zama bayinsu.
Mallam Sanusi Lamido ya kira Najeriya da ’yan Afrika su tashi daga barcin da su ke yi su sani cewa suna cikin wani hali wanda in ba a taka masa birki ba yanzu to, lallai za a yi da-na-sani a nan gaba.
Ya ce dole kasashen Afrika su farka su gane cewa wannan shirin na kasar Sin na sassaucin farashi da jula-jalar kudin kasarsu da yake yi wa kayansu hanya babban kalubale ne wanda in ba a dakile shi da wuri ba zai mai da mu bayinsu a cikin karamin lokaci.
In dai a na so wannan auren zoben ya dore to lallai dole su ‘yan kasar Sin su kafa wadannan masana’antun a Najeriya sannan a dauki ‘yan Najeriya su rika aiki, ko kasar nan ta rika samun kudin haraji ko a samu habakar tattalin arzikin kasa.
Lallai gwamnati da manya manyan ’yan kasuwarmu dole su hade kansu wajen dawo mana da martabarmu da kimarmu da ta zube warwas a idon duniya. An raina mu saboda ba ma iya tabuka komai yanzu. Ko tsinken sakatar hakori daga kasar Sin a ke shigo mana da shi.  
Wadannan mutane kada mu ji da wai su ba Afrika ko al’ummar Afrika ne a gabansu ba. Tunaninsu shi ne yaya za a yi su fadada karfin tattalin arzikin kasarsu, yaya za a yi su bunkasa cinikayyarsu da duniya, yaya za a yi su daga darajar al’ummarsu da kasarsu. Kada damar da suke da ita ta yi wa ’yan Afrika ’yar birin-birin ta dore kafin idanunsu su bude su ga irin ta’adin da ake yi musu.  Lokaci ya yi da Najeriya da Afrika za su farka, idan ba haka ba a yi musu sakiyar da babu ruwa.
Abdullahi A. Babayaro ya rubuto daga No.13 Isyaka Aliyu road, Mando Kaduna.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50