Sanya addini a siyasar Jihar Taraba ke hana ta ci gaba – Aaron Artimas
Mista Aaron Artimas shi ne mataimaki na musamman a kan harkokin watsa labarai na tsohon Mukaddashin Gwaman Jihar Taraba Alhaji Garba Umar, a hirarsa da wakilinmu ya maida martani kan batanci da zargin da jami’an gwamnantin Darius Ishaku ke yi kan gwamnanti Garba Umar: Aminiya: Kwanaki gwamnatin Jihar Taraba ta dakatar da ma’aikatan da aka […]
Mista Aaron Artimas shi ne mataimaki na musamman a kan harkokin watsa labarai na tsohon Mukaddashin Gwaman Jihar Taraba Alhaji Garba Umar, a hirarsa da wakilinmu ya maida martani kan batanci da zargin da jami’an gwamnantin Darius Ishaku ke yi kan gwamnanti Garba Umar:
Aminiya: Kwanaki gwamnatin Jihar Taraba ta dakatar da ma’aikatan da aka dauka aiki a zamanin gwamnatin Garba Umar ta ce saboda hukuncin Kotun koli ya ce gwamnantin da ya yi wa shugabanci haramtacciya ce don haka duk ayyukan da aka gudanar a lokacin mulkisa haramtatce ne, mai za ka ce kan wannan batu?
Mista Aaron: Ba inda Kotun koli a cikin hukuncinta ta ce gwamnatin Garba Umar haramtacciya ce, muna da kwafin shari’ar kuma mu ba jahilai ba ne. Abin da Kotun koli ta ce shi ne kwamitin da Majalisar Dokokin Jihar Taraba ta nada ya binciki zargin karya doka da aka yi wa Mataimakin Gwamna a wancan lokaci wato Alhaji Sani Abubakar danladi ya gudanar da bincikensa cikin gaggawa kuma ya mika rahotonsa ba tare da an ba wanda ake zargi isasshen lokaci ya kare kansa ba. Saboda haka sai Kotun kolin ta ce haka din ya saba wa doka wato ba a bi ka’ida ba wajen tsige shi, kuma ta bayar da umarnin cewa a maida shi kan mukaminsa na da. In ka dubi wannan hukunci ba inda aka ce majalisar ba ta da hurumin kafa wancan kwamiti da ya binciki zargin laifuffukan da aka yi wa Sani Abubakar danladi. Kuma kamar yadda kowa ya sani Alhaji Garba Umar ya zama Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba ne bayan majalisa ta tsige Alhaji Sani Abukabar danladi Kuma ba inda kotun ta ce gwamnatin Garba Umar haramtacciya ce domin ba shi ya kai kansa kan mukamin Mataimaki Gwamna ba, tsarin mulkin kasar nan ne ya tanadi haka, doka ce ta ba shi domin sai da aka kai sunansa majalisa kuma aka tantance sannan aka rantsar da shi. Kuma ya kamata jama’a su sani cewa ba inda tsarin dokokin kasar nan ya yarda cewa a jiha ko a tarrayya ko a karamar hukuma a zauna ba shugaba. Da zarar Shugaban kasa ko Gwamnan ko Shugaban karamar Hukuma ya kasance ba shi a kan kujerar mulki bisa dalilan rashin lafiya ko mutuwa ko kuma aka tsige shi daga kan mukaminsa, to dole ne mataimakinsa ya maye gurbinsa.
Haka muka samu kanmu a wannan jiha, Gwamna danbaba Suntai ya samu mummunan rauni a dalilin hadarin jirgin sama. Rashin lafiyar danbaba ya sa ba zai iya tafiyar da harkokin mulki ba .Wannan shi ya sa Majalisar Dokokin Jihar Taraba ta sake bi tsarin dokokin kasar nan ta nada Alhaji Garba Umar a matsayin Mukaddashin Gwamna don ya ci gaba da gudanar harkokin gwamnati har zuwa lokacin da mai gidansa zai samu lafiya ya dawo ya ci gaba da aikinsa.
To amma abin mamaki sai aka sanya maganar addini a cikin wannan lamari wanda tsarin mulki ya fayyace komai a kai, ta sharri tare da tunzura jama’a ta yadda za a dagula lamurra. A cikin wannan yanayi ne Alhaji Garba Umar ya gudanar da mulkinsa har zuwa lokacin da Kotun koli ta yanke hukuncin a maido da tsohon Mataimaki Gwamnan da majalisa ta tsige bisa mukaminsa na da.
Aminiya: Ka ce a cikin hukuncin Kotun koli ba inda aka haramta nada Alhaji Garba Umar a Mukaddashin Gwamna, to me ya sa ya bar kujerarsa?
Mista Aaron: Ka san shi Alhaji Garba Umar dattijo ne kuma mutum ne mai son zaman lafiya da wani ke kan kujerar mulki kotu ta yanke irin wannan hukunci da ba zai sauka ba illa kawai ya sake komawa Kotun kolin ya nemi a fassara wannan hukunci domin a hukuncin da ta zarta ba inda aka ce nadinsa ba a yi shi bisa doka ba, ko kuma aka haramta nadinsa. Wannan lamari ya ba ni mamaki domin muna da masu ilimin shari’a masu yawan gaske a jhar nan, amma saboda rashin gaskiya da nuna bambancin addini sai aka fadi abu daban da hukuncin da Kotun kolin ta zartar. A ka yi ta yada labarun karya cewa kotu ta sauke Garba Umar alhali kuwa kotu ba ta ce komai dangane da mukamin da yake kai ba.
Dole aka tilasta wa Garba Umar sauka daga mukaminsa mu na kusa da shi mun nemi ya ta tafi kotu don ya nemi kotu ta yi bayani kan wannan hukunci ya ce mana a bar wa Allah komai.
Aminiya: Wasu na mamakin yadda wadanda suka tsaya kai-da-fata wajen dole sai an tsige Sani Abubakar danladi su ne kuma suka dawo suka hadu suka tabbatar an dawo da shi kan mulki, a ganinka me ya kawo haka?
Mista Aaron: Wannan ba abin mamaki ba ne domin kowa ya ga yadda shi Alhaji Garba Umar ya samu karbuwa ga al’ummar wannan jiha, hakan ya faru ne a saboda saukin kansa da dattakunsa tare da salon mulkinsa na hada kan al’umma. Kuma ya kasance mutum mai tausayi wanda ba ruwansa da bambancin addini shi ya sa jama’a suka rungume shi. To wannan shi ya sa wasu gungun mutane da ke amfani da addini suka sa masa karan-tsana domin sun fahimci cewa in ba a cire shi daga mulki ba bukatarsu ba za ta biya ba. Shi ya sa bayan an cire shi daga mulki aka ki yarda a gudanar da zaben fidda-da-gwani na ’yan takarar Gwamna a nan Jalingo aka kai Abuja. Ka ga yadda jama’a suka tarbi Alhaji Garba Umar a lokacin da ya dawo Jalingo bayan ana sauke shi daga kan mukaminsa wannan ya nuna cewa duk da kasancewar ya bar karagar mulki amma jama’a na tare da shi. Yadda jama’a suka nuna kaunarsu gare shi, ya sa wannan gungun mutane suka ki shi domin sun gane cewa in an gudanar zabe na gaskiya a Jam’iyyar PDP a wancan lokaci ba wanda zai kayar da Alhaji Garba Umar. To a zahirin gaskiya wadanda suka kasance a gaba-gaba wajen tsige Sani Abubakar danladi su ne suka sake haduwa waje guda suka tsaya kai-da-fata a mai da shi bisa mukaminsa. Ba su yi haka da niyya mai kyau ba illa kawai don cimma burinsu na ganin wanda suke so ya zama Gwamna.
Aminiya: Yanzu ana zargin shigar da maganar addini a harkokin siyasar wannan jiha, a ganinka me wannan yanayi zai har haifar ga al’ummar jihar?
Mista Aaron: Wannan abu ne mai hadarin gaske, zai iya haifar da rashin zaman lafiya. Abin takaici ne yadda masu mulki a jihar nan suka cusa maganar addini a harkar siyasa da mulki. In ka lura sauran jihohin kasar nan sun wuce maganar addini da kabilanci, illa kawai yadda za a ciyar da jama’a gaba ta hanyar aiwatar da ayyukan raya kasa. Har yanzu jiharmu ce a baya in aka kwatanta da jihohin da aka kirkiro su tare, (ko a bayanta) kamar Jihar Gombe da ke makwabtaka da mu. Ci gaban da aka samu ta fuskar tattalin arziki da ilimi da gina hanyoyi, Jihar Gombe ta yi mana fintinkau, amma abin kunya sai ga shi ana fifita maganar addini a jiharmu.
Bari in koma da kai baya a lokaci mulkin Garba Umar ya kasance ana karancin malamai a mafi yawan makarantumu, misali a wasu makarantu za ka iske akwai dalibai sama da 1,500, amma malamai kasa da 10 ki koyarwa a makarantar. Wannan ya sa ya wajaba a dauki malamai, amma yanzu an ce ba a kyauta ba da aka dauki malaman, kuma dukkan wadanda aka dauka aikin ’yan jihar nan ne. Abu mai muhimmanci ga irin tafiyar da mu da muka yi aiki da Alhaji Garba Umar, Kiristoci da Musulmi har yanzu kanmu hade yake duk lokacin da wani abu ya taso sai ka ga mun hadu cikin dan karamin lokaci wannan ya nuna irin jagoranci mai kyau da shi mai gidanmu ya gudanar.
Aminiya: Amma wasu na ganin cewa ba wani abin a zo a ganI da Garba Umar ya aiwatar a lokacin mulkinsa, mene ne ra’ayinka kan wannan zargi?
Mista Aaron: To a tsari irin na dimokuradiyya kowa na da ’yancin fadin albarkacin bakinsa, sai dai kada ka manta komai kyan ayyukan da ka gudanar makiyinka zai ce ba ka yi komai ba. Ni na san cewa irin ayyukan alheri da Alhaji Garba ya gudanar a lokacinsa za a daukin shekaru masu yawa ana cin amfaninsu.
dauki aikin gyaran hanyar da ta tashi daga Jalingo ta bi ta Sunkani ta wuce garin Bali har Serti zuwa Gembu, wannan aiki danbaba Suntai ne ya kirkiro shi amma Alhaji Garba Umar ne ya bayar da shi ya kuma biya kudin aikinsa sama da Naira biliyan takwas. Yanzu an kammala wannan aiki sauki ya samu ga al’ummar kananan hukumomi sama da shida da ke amfani da hanyar. Kuma a lokacinsa ne aka biya sama da Naira miliyan 500 don bunkasa ayyukan kafa masanaantu da ’yan jihar nan za su ci moriyar shirin. Kuma an yi shekaru masu yawan gaske ba a b dalibai kudin tallafi (scholarship), amma ya biya duk kudin da daliban ke bi.
Za a dauki lokaci mai yawa in aka ce za a lissafa irin ayyukan alherin da Alhaji Garba Umar ya gudanar, kuma mafi alheri daga cikin ayyukan shi ne kawo zaman lafiya da kawar da bambancin addini wanda yanzu kuma ake ruruta gabar addini a tafiyar da ake yi. Sai dai ya kamata wadanda suka kawo maganar addini a siyasar jiharmu su sani Allah zai kama su, domin ba za ka yi wa Allah karya ka kwana lafiya ba, Allah zai kama irin wadannan mutanen nan ba da dadewa ba.