Sanya ido kan mutum 50 ya yi daidai – Pasali

Alhaji Danladi Garba Pasali shi ne Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta Buhari Campaign Organization na Kasa. A tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya ce umarnin da Shugaba Buhari ya bai wa jami’an tsaro kan su sanya ido a kan wadansu mutane 50 da ake zargi da handame dukiyar Najeriya, […]

Sanya ido kan mutum 50 ya yi daidai – Pasali

Alhaji Danladi Garba Pasali shi ne Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta Buhari Campaign Organization na Kasa. A tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya ce umarnin da Shugaba Buhari ya bai wa jami’an tsaro kan su sanya ido a kan wadansu mutane 50 da ake zargi da handame dukiyar Najeriya, don ganin ba su fice daga kasar nan ba, ya yi daidai. 

 

Aminiya: Me za ka ce kan sunayen mutum 50 da gwamnati ta bai wa jami’an tsaro umarnin su sanya ido a kansu don ganin ba su fice daga kasar nan ba?

Pasali: Wannan mataki da gwamnatin Najeriya ta dauka yana daga cikin abubuwan da duk wani mai kishin Najeriya yake son ganin Shugaba Buhari ya yi. Domin ’yan Najeriya sun zabi Shugaba Buhari ne domin ya duba wadannan matsaloli. Domin cin hanci da rashawa ne ya jefa kasar nan cikin mummunan halin da take ciki. Ya kashe kasar nan ya kawo rigingimu iri-iri, ya haifar da ’yan fashi da makami da ’yan tawaye da rashin adalci da rashin kirki  da kwashe dukiyar kasar nan. Kuma idan ka tuna Shugaba Buhari ya sha fadi cewa, ya zo ne domin ya yi gyara kan wannan matsala ta cin haci da rashawa.

Kowa ya san Buhari ba mai dibar dukiyar jama’a ba ne, domin duk da ya yi Minista da Gwamna da Shugaban Kasa, kowa ya shaide shi bai ci kayan kowa ba. Saboda haka wannan umarni da Shugaba Buhari ya kawo dama doka ce da take cikin kundin tsarin mulkin kasar nan. Domin idan ka tunA wata 6 da suka gabata ne aka fito da wannan doka. Mutane suka yi ca aka samu wadansu suka tafi kotu.

Yau baki daya bai fi kwana uku ba, Shugaba Buhari ya kaddamar da wannan doka. Bayan da kotu ta tabbatar masa da wannan izini. Dama akwai mutane da suke da shari’a a gaban kotuna da hukumomin EFCC da ICPC. Haka kuma akwai mutanen da ake zargi cewa sun rarumi dukiyar kasa a Najeriya.

A kasashe irin su Ghana kowa ya ga irin yadda tsohon Shugaban Kasar J.J. Rawlings ya jera wadanda suka sace kudaden kasar ya kashe su. A kasar China kashe duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa ake yi.  Ai a Najeriya Shugaba Buhari ya yi adalci da ya ce a zuba wa wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa ido ne, don kada su fice daga kasar nan, saboda suna karkashin bincike. Don haka ni ban ga wani abin damuwa ba, kan wannan al’amari.

Aminiya: Wadansu suna zargin cewa gwamnati Buhari ta dauki matakin ne don ganin zaben shekara ta 2019 ya gabato?

Pasali: Ai shi ne na ce maka fiye da wata 6 ke nan da kafa wannan doka. Bayan kafa wannan doka wadansu sun tafi kotu, don haka ban ga wani laifi ba, kan wannan mataki da Shugaba Buhari ya dauka. Kuma duk wanda ya san Buhari tun a lokacin yakin neman zabensa ya fadi cewa zai yaki cin hanci da rasha a kasar nan.

Martabashi da ake yi a kasashen duniya ana yin haka ne saboda wannan dalili na yaki da cin hanci da rashawa da yake yi. Domin duniya ta yarda shi ba barawo ba ne kuma ba azalumi ba ne.

Bari in ba ka wani misali duk dan Najeriya da ya je Saudiyya ko Ingila ko Amurka duk inda aka yi cinikin da ya kai Dala dubu 10, sai an binciki mutumin da ya yi wannan ciniki. Ko mota mai kyau aka ganka da ita kana yawo, sai an bincike ka.

Kuma idan ka duba a shari’ar da aka yi a kwanakin baya mutanen da aka fara daurewa kan cin hanci da rashawa a kasar nan ’yan Jam’iyyar APC ne, wato tsohon Gwamnan Jihar Filato Joshua Dariye da tsohon Gwamnan Jihar Taraba Joly Iyame. Don haka duk wani mai hankali da ya san Shugaba Buhari yana yin wannan yaki ne, saboda dalilin da ya sa ya fito takarar Shugabancin Kasar nan ke nan.

Aminiya: To yanzu ga shi Jam’iyyar PDP ta tsayar da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar a matsayin dan takarar Shugaban Kasa, ba ka ganin zai iya kayar da Shugaba Buhari a zaben da za a yi?

Pasali: Abin da nake son ka gane shi ne mu murna muke yi da Jam’iyyar PDP ta tsayar da Atiku Abubakar, saboda mun san an kawo mana wanda za mu yi masa mummunar kaye ne a zaben da za a gudanar. Saboda ina son in tabbatar maka cewa Atiku Abubakar mutum ne da ya yi shekara 8 yana Mataimakin Shugaban Kasa. Don haka ina tabbatar maka cewa fitowar Atiku Abubakar a wajenmu mu da muka san wane ne Atiku mun san garabasa za mu samu.

Yau idan ka tashi daga Gombe a mota ka ce kana so ka je Yola babban birnin Jihar Adamawa wato jihar Atiku, hanyar babu kyau. Saboda haka mutumin da bai iya gyara jiharsa ba, babu abin da zai yi idan ya zama Shugaban Najeriya.

Wato wannan wani zabe ne za a yi, tsakanin gaskiya da karya.

Aminiya: Wane sako ko kira ne kake da shi ga al’ummar Najeriya?

Pasali: Sakon da nake shi ga ’yan Najeriya shi ne lokaci ya zo da za su bai wa Shugaba Buhari goyon baya a wannan zabe mai zuwa. Al’ummar Najeriya su tabbatar sun dawo da Shugaba Buhari kan shugabancin kasar nan don a samu adalci, a sake samun ci gaba a kasar nan. Kowa ya san cewa hawan Buhari mulkin kasar nan shekara 3 da rabi da suka gabata, ya sake farfado da jiragen kasa a Najeriya. Hanyoyin da a da ba su da gyara yanzu yana gyara su. Ga aikin wutar lantarki na Mambila a Jihar Taraba da sake farfado da kamfanin mulmula karafa na Ajaokuta. Ga farfado da aikin gona a kasar nan, yau mutanen Najeriya babu ruwansu da maganar sayo shinkafa daga waje, yanzu ana fitar da kayayyakin amfanin gonar da aka noma a Najeriya zuwa kasashen waje. Ga maganar tsaro, a da kowa tsoron shiga masallaci ko coci ko kasuwa da tashoshin mota yake yi a Najeriya, saboda tsoron tashin bama-bamai. Don haka zaben Shugaba Buhari da al’ummar Najeriya suka yi alheri ne ya kawowa kasar nan.