Sanya kakin agaji ya jefa 442 a komar hukuma

Mubarak dai fitaccen mawaki ne da aka fi sani da Mr 442, inda yake wakokin gambara da Ingausa.

Sanya kakin agaji ya jefa 442 a komar hukuma

Wani matashi mai suna Mubarak Abdulkarim, wanda aka fi sani da 442 wanda mawaki ne a Zariya ya shiga hannun hukuma bisa zarginsa da laifin sojan gona a matsayin dan agajin Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS).

Da yake bayanin abin da ya aikata ga Jaridar Aminiya, mawaki Mubarak ya ce ya sanya kakin agaji na JIBWIS ne ya yi bidiyo, inda ya yi kira ga ’yan agajin Izala su fito su bayar da gudunmawa a lokacin zanga-zanga.

Ya ce ya samu kakin a dakin abokinsa wanda dan agajin ne da ya yi gugar kayan ya tafi ya yi wanka sai ya sa ya yi bidiyo ya tura a kafar sada zumunta.

Mubarak Abdulkarim ya ce shi mazaunin Hanwa ne a Karamar Hukumar Sabon Garin Zariya kuma yana sana’ar waka ce.

A yayin da matashi Mubarak ke bayyana nadamarsa, ya nemi gafarar JIBWIS da Daraktan Agaji na Kungiyar na Kasa da daukacin ’yan agaji na kungiyar tare da yin alkawarin ba zai sake aikata makamancin haka ba.

Matashin mawakin ya yi alkawarin zai yi rajista a matsayin dan agaji domin shi ma ya bayar da tasa gudunmawar ga ci gaban addinin Musulunci.

An kama Mubarak ne a Zangon Shanu da ke Jama’a Zariya bayan da mutane da dama suka nuna damuwa kan bidiyon da ya yi, musamman ganin cewa an san shi a mawaki ba dan agaji ba.

Da yake bayani kan lamarin Barrista B. Jafaru ya ce Mubarak ya aikata laifin yin sojan gona kasancewar shi ba dan agaji ba ne.

Barrista Jafaru ya ce yanzu matakin da Kungiyar Izala za ta dauka shi ne za ta kafa kwamitin da za a zauna da shi domin yi masa wa’azi da nasiha a kan yadda yake tafiyar da rayuwarsa domin ya canja zuwa rayuwa ta kwarai.

Waiwaye a kan Mubarak

Mubarak dai fitaccen mawaki ne da aka fi sani da Mr 442, inda yake wakokin gambara da Ingausa.

Ba yau ya fara ta da kura ba kasancewar a watan Nuwamban 2022 hukumomin Jamhuriyar Nijar suka sanar fara bincike kan yadda shi 442 din da abokinsa Ola suka mallaki takardun kasar na bogi da aka kama su da su.

An tsare su a gidan yarin birnin Yamai inda suka zauna tsawon lokaci kafin su samu fitowa su dawo Nijeriya.

Babban mai shigar da kara na kasar a lokacin da ake tsare da su ya bayyana cewa sun mallaki takardun bogi ne, wanda kuma babban laifi ne a kasar.

Bayan dawowarsu, 442 ya ce sun yi niyyar tafiya kasar waje ne, wanda hakan ya sa suka yi yinkurin amfani da takardun kasar Nijar, amma wani ya damfare su, ya hada musu takardun bogi, har suka shiga hannu.

Alakarsa da Safara’u

A daya bangaren kuma, mawakiya Safa, wato Safara’u ta Kwana 90 wadda ta koma waka bayan ta daina fim, ta fada cikin hadakar mawakan ne, inda ta rika ta da kura da wakokin da suke yi tare da 442.

Sai dai bayan an kama su a Nijar ne aka lura ta dan ja baya da su, wanda har yanzu babu alamar sun daidaita.

A wata hirarta da Hadiza Gabon, Safa ta bayyana cewa 442 ya taimaka mata wajen jawo ta a jiki, sannan ta bayyana cewa mutumin kirki ne, wanda ba ya wasa da Sallah sannan yana son Sanya kakin agaji ta jefa 442 a komar hukuma Mawaki Mubaraka Abdulkarim (Mr 442) taimakon mutane.

Sai dai bayan ya dawo, ya yi wata waka da aka yi tunanin gugar zana yake mata, inda a ciki yake nuna cewa ya taimaka mata, amma ta yi watsi da shi.

Daga baya a tattaunawarsa da BBC ya bayyana cewa ya taimaka mata ne a lokacin da take matukar bukatar taimakon kasancewar ya daina fitowa a fim.