Sanya siyasa a batun sace ’yan matan Chibok ya jawo matsala – Sanata Abu Ibrahim
Sanata Abu Ibrahim na Jam’iyyar APC daga Jihar Katsina shi ne Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa, a tattaunawarsa da manema labarai, ya tabo lalacewar al’amuran tsaro a kasar nan, inda ya zargi Gwamnatin Tarayya da sanya siyasa a cikin batun sace ’yan matan Chibok: Aminiya: A halin yanzu batun tsaro ne ya fi damun […]
Sanata Abu Ibrahim na Jam’iyyar APC daga Jihar Katsina shi ne Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa, a tattaunawarsa da manema labarai, ya tabo lalacewar al’amuran tsaro a kasar nan, inda ya zargi Gwamnatin Tarayya da sanya siyasa a cikin batun sace ’yan matan Chibok:
Aminiya: A halin yanzu batun tsaro ne ya fi damun kowa a kasar nan, shin a majalisa kun gamsu da matakan da ake dauka don magance matsalar ko kuna ganin akwai abubuwan da ya kamata a yi da ba a yi?
A ’yan kwanaki da suka wuce manyan sojoji da masu kula da tsaron kasa kamar shugaban ’yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya da shugabannin sojojin ruwa da na sama sun zo mun zauna da su a matsayinmu na shugabannin majalisa. Mun kuma ji batutuwan da ba za su iya fadi a gaban mutane ba, mun ji koke-koke da matsalolinsu. Don haka a yanzu babban matsalar da ta damu Najeriya ita ce batun Boko Haram da kuma ta ’yan mata da aka sace. A fahimtata, su kansu suna da matsalolinsu, misali ko an ce ga kudin da za a ba su, su biya alawus da albashin soja sai ka ga an dade ba a ba su ba. Idan kuma ba a ba su ba, babu yadda za a yi su ba na kasa. Na biyu akwai rashin kayan aiki, yanzu duniya ta ci gaba saboda haka ba sai ka shiga daji ba. Za ka iya amfani da na’ura wajen gano mutanen da suka wuce biyu, amma ba su da irin wadannan kayayyaki. Na uku sojan yanzu ya sha bambam da na baya, na da yana shiga soja ne saboda yana sha’awar aikin, amma yanzu da yawa suna shiga soja ne saboda ba su da aikin yi. Wanda ya shiga soja saboda sha’awa yana iya zuwa yaki ba tare da tsoro ko shakku ba. Amma wanda ya shiga saboda rashin aikin ba zai iya jajircewa ba. Yanzu haka a Maiduguri akwai ’yan kato da gora matasa da suka tashi don kashin kansu su kare garinsu. Sai muka ce me zai hana sojoji su dauke su aiki, a dauke su a kuma koyar da su. Misali a dauki kamar matasa dubu biyar a jihohin Yobe da Borno da Adamawa, a ga in ba su shiga dajin Sambiza ba. Saboda haka muna nan muna duba yadda za a yi a matsayinmu na ’yan majalisa. Ga kuma shigowar kasashen waje kan wannan batu, dole sai an cika wasu ka’idoji da za su yarda su tsaya domin yin wannan aiki. Wannan abu da ke faruwa zai sa a tashi tsaye wajen magance matsalar. Kwanan nan Shugaba Jonathan da shugabanni makwabata Najeriya suka taru a kasar Faransa domin tattauna yadda kasashen Afirka za su hada kai wajen kawo karshen matsalar. A kullum ina cewa idan har ba mu hada kai da kasashen Nijar da Kamaru da Chadi ba, muna da matsala. A yanzu haka ’yan Boko Haram suna bakin iyakokinmu, a nan suke gudanar da ayyukansu. Ka ga idan aka hada kai zai taimaka matuka, kuma ga alama taron da aka yi zai kawo hadin kai a tsakaninmu da sauran kasashen Afirka makwabta.
Aminiya: Ana ci gaba da neman ’yan matan da aka sace, kuma ana gudanar da zanga-zanga a kasashen duniya. Shin a iya cewa sun gagari jami’an tsaron Najeriya ne aka koma dogaro da kasashen ketare?
Gaskiya duk da cewa mutane na cewa ba a son kawo siyasa cikin wannan lokaci, amma a siyasance Gwamnatin Tarayya ta yi sakaci kwarai da gaske. Kowa ya san farkon abin nan wasu na ganin karya ne wai so ake a bata sunan Jonathan. Mun ga yadda matarsa ta fito tana ihu tare da yin wasu abubuwa da ba su kamata ba. Tunda farko kafin awa 48 ya kamata a san abin da ake ciki, amma sai aka bata lokaci a kan gaskiya ne ko ba gaskiya ba ne. Abin na da ban mamaki wai wanda ke mulkin Najeriya ba zai iya sanin cewa tabbas abin ya faru ko bai faru ba. Kamar yadda na ce duk da ba a son a kawo siyasa cikin lamarin, ba siyasa ba ce gaskiya ce. kila za a ce don ba na cikin PDP shi ya sa nake fadin haka. To, amma gaskiya daya ce kuma wallahi ko ina cikin PDP zan fadi gaskiya. Saboda kasarmu ce kuma sunanmu ke baci a duniya, akwai jami’an tsaro su za su iya fada maka an yi ko ba a yi ba. Wannan ya riga ya faru kuma sojojinmu suna da karancin kayayyaki. Yaran nan an sace su kuma ba za ka tashi da sojojin nan ka ce za ka je ka kwato su ba sai su kashe su. Idan ana son kwato su, dole sai an bi ta na’ura wadda za ta nuna a ina suke sannan sai an bi ta yadda za a yi magana da wadanda suka kama su domin kada su halaka su. Ina ganin matsala ce wadda ba mu saba da ita ba ta faru, kuma ba mu da na’urorin zamani da za su taimake mu gano inda suke, yanzu kasashen waje sun zo da wadannan abubuwa.
Aminiya: Ba ka ganin idan sojojin waje suka kubutar da ’yan matan, darajar sojojin Najeriya za ta zube?
Idan abu ya taso mafita ake nema, mafitar kuma ko ta yaya dole a neme ta kuma dole ne mu yarda cewa Najeriya na cikin kasashe masu tasowa. Abin da sojan Ingila ko na Amurka zai yi ko kafarsa ba za mu kama ba. Wannan ne ma zai kara wa mu ’yan Najeriya kaimin ba sojojinmu abin da ya kamata, tunda ba mu ba su abin da ya kamata mu ba su. Wannan zai nuna mana rashin karfinmu a waje kaza kuma ya kamata mu yi kaza a waje kaza.
Aminiya: Shin ba a ba sojoji abin da ya kamata ne domin babu ko ba a ba su ne domin wata manufa?
Gwamnati ita ta fi sanin inda ya fi yi mata zafi, kuma ga shi ba na cikin gwamnatin, ina cikin masu cewa ne a duba kasafin kudinta. A ganina muna kashe kudi masu yawa ga sojoji ne wajen biyan albashi da alawus amma ba mu kashe kudi wajen al’amuransu na yau da kullum. Ina cikin kwamitin ’yan sanda kuma idan ka ga kudin da ake ba DPO don shan mai a wata bai wuce Naira dubu hudu ko biyar ba. Wanda shi ne zai rika zagayawa domin ganin mai ake ciki. Ka ba shi kudin man kwana daya, sauran a cikin aljihunsa zai cika? Ga motocin nasu ba a kulawa da su duk sun lalace sannan kudin man babu, ta yaya zai yi aikin. Babu bindigogi ballantana mutanen da zai yi aiki da su, muna ganin kudin da ake ba su sun yi karanci matuka. Za ka ji a misali an ce an ba soji dubu, Naira miliyan 800 duk kudin albashi ne. Yanzu abin da nake ji a wajen abokan aikinmu shi ne dole a rika ba sojojin abin da ya kamata a ba su idan muna son zama lafiya.
Aminiya: Kawo sojojin ketare a bangarenku na ’yan Adawa kun amince?
Ba fa sojoji aka kawo Najeriya ba, su kasashen wajen jami’ansu za su aiko da kayan aiki da na’urorinsu domin taimaka mana. Babu wanda ya aiko da sojansa na kasa da zai shiga dajin Sambiza a yi yaki, wannan ne dole sai an yi shawara da mu. Amma domin a kawo masana da kayan aiki wannan hakkin gwamnati ne kuma saboda rayukan wadannan ’yan mata ina ganin duk abin da za a yi domin ceto su daidai ne.
Aminiya: Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shikau ya yi tayin cewa a shirye suke su yi musayar fursunoni da gwamnati. Shin kana ganin yin hakan ya dace?
Gwamnati ita ta san abin da take ciki, domin ita ke da jami’an tsaro, ita ta san mai za ta iya yi. Kuma shin ta tabbatar da ta san inda ’yan matan suke idan har ta tabbatar da inda suke tana iya amincewa domin kubutar da rayuwarsu. Amma idan ba ta sani ba, ta san maganar banza ce. Saboda haka wannan wani abu ne da nake ganin gwamnati dole ta yi taka-tsantsan a tabbatar cewa ’yan matan na nan. Na biyu a ina suke, kuma shin Shikau din ma shi ne ko kuwa wani ne daban. Shin mai maganar da gaske yake ko a’a saboda ya ga duk duniya ta tasar musu ne, har Alka’ida an ce ta ce ba ta sace mata ko kashe mutane da kona makarantu da dukiyoyi. Idan har aka ne ka ga ke nan shi Shikau din idan ma yana nan shi kadai yake abinsa. Saboda haka abubuwa da yawa za a duba. Ni a matsayina na Sanata akwai abubuwa da yawa da ba su a gabana, amma ita gwamnati da ke da jami’an tsaro da masu ba da shawara a kan tsaro ita ya kamata ta zauna ta duba wadannan abubuwa.
Aminiya: A kwanakin baya batun rashin tsaro ya faru a mazabarka inda aka halaka mutane masu yawa, ko akwai alaka da Boko Haram?
Ga abin da na fahimta da tattaunawar da muka yi akwai wadanda ake zargi da cewa ’yan Boko Haram ne da suka shigo, sannan kuma akwai wasu da ake ganin ’yan kasar Mali ne da suka shigo ta wajen Katsina da Birnin Gwari da Zamfara. Jami’an tsaro na nan na ci gaba da binciken masu hannu a ciki. Sojoji na nan sun shiga dajin suna aiki domin na je wajen kwanan nan. Na je ne domin in kai musu taimako amma sai na ga jama’ar da suka taru a wajen abin ya ba ni mamaki. Wanda alama ce da ke nuna al’umma sun fara koma gidajensu. Na tallafa musu da injunan ban ruwa domin ci gaba da rayuwansu na noma domin akasarinsu ba su da shanu a yanzu a sace. Zan sayo kamar injuna 200 domin raba wa mutane. Amma dai na rigaya na raba musu 25 kafin sauran so iso.
Aminiya: An zabe ka sanata har sau uku, ko za ka fada mana nasarorin da aka samu wajen inganta rayuwar mutanenka?
Na gode wa Allah domin zan ce akwai manyan ayyuka musamman na hanyoyi guda biyar da na samo daga Gwamnatin Tarayya ana kuma yi. Akwai aikin madatsar ruwa ta Kafur da na iske ana yi amma mu muka kammala ta. Akwai madatsar ruwa ta Musawa da na Faskari. Game da makarantu kuwa na tabbata babu karamar hukumar da ba mu gina makaranta ba a kananan hukumomin 12. Mun sayi taransfomomi 23 kuma kowace karamar hukuma mun ba ta nata, mun kuma yi rijiyoyin burtsatse mun kuma yi rijiyoyin ban ruwa dubu daya da dari daya, kowace karamar hukuma an yi guda dari inda kuma aka yi rijiyar an ba su injunan ban ruwa. Kwanakin baya mun raba kayan sana’o’i ga matasa, akalla matasa 450 muka ba a kananan hukumomi 11. Ayyuka ne da suka hada da nawa da na Gwamnatin Tarayya.