Sanya siyasa a rashin lafiyar Buhari sakarci ne – Yahaya Kwande
‘Buhari zai dawo a makon gobe’ Jigo a Jam’iyyar APC ta Kasa kuma babban jigon jam’iyyar a Jihar Filato, Ambasada Yahaya Kwande ya ce sakarkaru wadanda ba su san mece ce siyasa ba suke sanya siyasa kan rashin lafiya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari har ta kai suke kiraye-kirayen ya yi murabus daga shugabancin Najeriya. […]

‘Buhari zai dawo a makon gobe’
Jigo a Jam’iyyar APC ta Kasa kuma babban jigon jam’iyyar a Jihar Filato, Ambasada Yahaya Kwande ya ce sakarkaru wadanda ba su san mece ce siyasa ba suke sanya siyasa kan rashin lafiya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari har ta kai suke kiraye-kirayen ya yi murabus daga shugabancin Najeriya.
Ambasada Yahaya Kwande wanda tsohon Jakadan Najeriya ne a kasar Switzerland ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilin Aminiya a gidansa da ke Jos a ranar Litinin da ta gabata.
Ambasada Kwande wanda yana daya daga cikin mutum 38 da suka kafa Jam’iyyar PDP a 1998, ya bayyana cewa duk da rashin lafiyar Shugaba Buhari ya ba shi maki 80 cikin 100 na nasara a shekara biyu da ya yi yana rike da mukamin Shugaban Kasa.
Ambasada Yahaya Kwande mai kimanin shekara 88 ya ce abin takaici ne a rika hada Buhari da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, inda ya ce “Ko da girgiza kurna ta fi magarya.”
Ya ce, “Shugaba Buhari ya yi kokari sosai, na ba shi maki 80 cikin 100 duk da rashin lafiyar da ke addabarsa. Idan ka dubi man fetur ya wadata a kasar nan, inda a shekarun baya mutum ba zai yi mafarki za a kawo karshen karancin man fetur ba. Jarumtar da Buhari ya yi na kawo karshen tallafin man fetur ne ya kawo haka.”
Ya kara da cewa a lokacin mulkin Jonathan mayakan Boko Haram sun ci karensu babu babbaka, inda har suka kwace yankunan da girmansu ya kai jihohi uku na Kudancin kasar nan, amma yanzu kowa ya san an ci karfinsu, domin mutane suna zuwa kasuwanni da wuraren ibada, sannan su yi barci cikin kwanciyar hankali ba tare da tunanin za a kawo musu hari ba.
Ya ce, “Dangane da batun masu kunar bakin wake kuwa hakan yana nufi mayakan Boko Haram karfinsu ya kare, tunda suka koma kai hare-haren kunar bakin wake.”
Ya nanata cewa yaki da cin hanci da rashawa da Buhari yake yi yana haifar da da mai ido, inda ya ce a yanzu gwamnati ta iya kwato biliyoyin Naira da Dala a wurin wadanda suka yi sama-da-fadi da kudin kasar nan. Ya ce nan gaba kadan talakawan kasar nan za su ga amfanin wadannan kudade da aka kwato.
Ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da yi wa Shugaba Buhari addu’ar samun lafiya, sannan ya kwankwashi masu tarere da rashin lafiyar Buhari cewa kowane dan Adam zai iya kamuwa da cuta. “Ina so su sani rashin lafiya da mutuwa na Allah ne, amma mutanen da ke terere da rashin lafiyar Buhari ba su da tausayi da imani, ya kamata su sani hakan da suke yi ba siyasa ba ce, kidahumanci ne,” inji shi.
Kalaman na Ambasada Yahaya Kwande suna zuwa ne a daidai lokacin da wasu manyan majiyoyi a Fadar Shugaban Kasa suka shaida wa Aminiya cewa ana sa ran Shugaba Buhari ya dawo Najeriya a makon gobe.
Majiyar Gwamnatin Tarayyar wadda ta nemi a sakaya sunanta wadda ta shaida wa Aminiya haka a ranar Talata da daddare ba ta fayyace a wace rana zai dawo a mako mai zuwan ba.
Majiyar ta yi magana ne ’yan awanni bayan da Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina ya shaida wa manema labarai cewa ba ya da labari kan yaushe Buhari zai dawo.
Shugaba Buhari yana hutun jinya ne a Ingila tun ranar 7 ga Mayun da ya gabata. Kuma daya daga cikin majiyoyin ya ce: “An shaida mana mu zauna cikin shiri domin dawowar Shugaban Kasar a mako mai zuwa. An kintsa komai a yanzu domin haka.”
Wata majiya kuma ta ce: “Muna cike da kyakkyawar fatan cewa Shugaban Kasa zai dawo a makon gobe. Wannan shi ne kawai abin da zan gaya muku a yanzu.
Da farko a ranar Talatar Kakakin Shuagba Buhari Femi Adesina ya shaida wa manela labarai cewa Shugaba Buhari ya shaida wa takwaransa na kasar Guinea Alpha Conde cewa yana samun sauki sosai, amma ba zai dawo ba sai likitocinsa sun ya yi haka.
Adesina ya ruwaito Buhari yana cewa a cikin wata wasika ta ranar 24 ga Yuli da ya rubuta wa Shugaban Guinea Alpha Code yana yi masa godiya kan addu’o’in kasa da mutanen Guinea suka shirya don nema masa lafiya.
A hira ta tarho da Shugaban Kasar Guinea Alpha Conde, Shugaba Buhari ya yaba wa al’ummar kasar bisa addu’ar da suka yi masa ta samun lafiya a makon jiya. “Na muku gode bisa halin kirki da hangen nesanka wajen shirya addu’o’in kasa baki daya don neman Allah Ya ba ni lafiya. Karimci ne da har abada zan rika tunawa da kuma yin alfahari da shi,” Adesina ya ruwaito Buhari yana fadi a cikin wasikar.
“Mai girma Shugaban Kasa, za ka yi farin ciki da jin cewa ina kara samun lafiya, kuma da zarar likitoci sun ba ni shawara, zan koma kan ayyukana, in ci gaba da hidima ga al’ummar Najeriya da suka zabe ni, kuma a kullum suke yi mini addu’o’in samun sauki,” inji wasikar.
Adesina ya ce Shugaba Buhari ya kuma amince da zabarsa ya jagoranci taron Tarayyar Afirka mai taken: “Yaki da cin hanci da rashawa a taron Tarayyar Afirka na shekarar 2018,” wanda shugabannin kasashen kungiyar suka yi a wani taronsu karo na 29 ranar 4 ga watan Yuli a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
Bayan da gwamnoni hudu da suka hada da Gwamnan Jihar Imo, Mista Rochas Okorocha da Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Jihar Nasarawa da Gwamna Nasir El-Rufa’i na Jihar Kaduna da kuma Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi da Shugaban Jam’iyyar ta Kasa Cif John Oyegun da Ministan Sufuri, Mista Rotimi Ameachi suka ziyarci Shugaban Kasar a farkon wannan mako, wadansu gwamnonin da suka hada da Shugaban Majalisar Gwamnonin Najeriya, Alhaji Abdul’Aziz Yari na Jihar Zamfara da Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima da Abdullahi Umar Ganduja na Jihar Kano da Udom Gabriel Emmnuel na Akwa Ibom da Abiola Ajimobi na Oyo da Dabid Umahi na Ebonyi ma sun je Landan a shekaranjiya Laraba.
Kakakin Shugaban Kasa Garba Shehu ya ce manufar ziyarar ta gwamnonin ita ce su isar da fatan alherin ’yan Najeriya ga Shugaban Kasar
Gwamnan Jihar Imo kuma Shugaban Majalisar Gwamnonin APC, Mista Rochas Okorocha ya shaida wa
Mista Okorocha, wanda ke daga cikin gwamnoni hudu da suka ziyarci Shugaba Buhari, ya shaida wa BBC cewa “Muna ganin daga nan zuwa mako biyu insha Allah zai koma gida ya ci gaba da aikinsa.”
Gwamna Okorocha ya kara da cewa Shugaban Kasar yana cikin koshin lafiya, “Kuma zancen da ake yi cewa yana cikin mawuyacin hali ba gaskiya ba ne. Yana nan lafiya lau. Na yi mamakin yadda na gan shi. Yana da koshin lafiya. Abubuwan da ake cewa game da rashin lafiyarsa ba haka muka gani ba,” in ji Gwamna Okorocha.
A cewar Mista Okorocha sun dauki kimanin sa’a guda suna liyafa tare da Shugaba Buhari a bayyanarsa ta farko a bainar jama’a tunda ya tafi jinya a birnin Landan kwana 80 da suka gabata.
Ya kara da cewa, “Shugaba Buhari ya gaya mana cewa da zarar likita ya sallame shi zai komo gida. Kuma da ni ne likitan zan sallame shi ganin yadda jikinsa ya yi kwari.”
A cikin wata sanarwa da ya fitar dangane da wannan ganawar, Kakakin Shugaban Kasa Femi Adesina ya ambato Gwamna Rochas Okorocha yana cewa Shugaban na cike da annashuwa kuma har yanzu yana nan da halinsa na yin raha da mutane.
Gwamnan ya ce tawagar tasu ta dauki kimanin sa’a daya tana liyafa da Shugaban Kasar, kuma inji shi daga tattaunawar da suka yi ga dukan alamu yana sane da duk abubuwan da suke faruwa a gida Najeriya.
Mista Okorocha ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna farin cikinsa da ziyarar tasu kuma ya tambayi kowanne daga cikin gwamnonin abin da ke faruwa a jiharsa.
Sanarwar ta ce da suka nemi jin abin da zai ce game da suka da miyagun kalaman da wadansu ’yan kasar ke furtawa game da halin da yake ciki, sai ya yi dariya kawai tare da bayyana abubuwan da ake fada a zaman karairayi. Ya ce abin da Shugaban ke jira kawai shi ne likitocinsa su ba shi dama ya dawo gida.
Ziyarar gwamnonin ta zo ne kwana 12 bayan da Mataimakinsa – wanda ya bar wa rikon kasar nan – ya kai masa wata gajeruwar ziyarar kuma ya shaida wa al’ummar kasar nan cewa mai gidan nasa na samun sauki cikin sauri kuma zai dawo ba da jimawa ba.
Rashin lafiyar Buhari tun farkon bana:
· 19 ga Janairu – Ya tafi Birtaniya domin
‘hutun jinya.’
· 5 ga Fabrairu – ya nemi Majalisar Dokoki ta
kara masa tsawon hutun jinyar.
· 10 ga Maris – Ya koma gida, amma bai fara
aiki nan take ba.
· 26 ga Afrilu – Bai halarci zaman Majalisar
Ministoci ba kuma ’yana aiki daga gida.’
· 28 ga Afrilu – Bai halarci Sallar Juma’a ba.
· 3 ga Mayu – Bai halarci zaman Majalisar
Ministoci ba a karo na uku.
· 5 ga Mayu – Ya halarci Sallar Juma’a bayan
mako biyu.
· 7 ga Mayu – Ya koma Birtaniya domin
jinya.
· 25 ga Yuni – Ya aiko wa ’yan Najeriya sakon
murya.
· 11 ga Yuli – Osinbajo ya gana da shi a
Landan.