Sanya siyasa a rikicin manoma da makiyaya ke kawo ta’azzararsa – Farfesa Dadari
Aminiya: Yaya kake kallon rikicin Fulani makiyaya da manoma da ke faruwa a jihohin Benuwai da Taraba? Farfesa Dadari: Rikicin Fulani makiyaya da manoma da ke faruwa yanzu a Najeriya, rikicin ne da yake da alaka da siyasa. Domin tuntuni makiyaya da manoma suke zaune tare, to amma a wannan yanayi da muke ciki an […]
Aminiya: Yaya kake kallon rikicin Fulani makiyaya da manoma da ke faruwa a jihohin Benuwai da Taraba?
Farfesa Dadari: Rikicin Fulani makiyaya da manoma da ke faruwa yanzu a Najeriya, rikicin ne da yake da alaka da siyasa. Domin tuntuni makiyaya da manoma suke zaune tare, to amma a wannan yanayi da muke ciki an zo an sanya siyasa cikin al’amuran makiyaya da manoma. Yanzu da ake maganar a koma ga yin noma da takin juji ko kashin shanu, ya kamata a gyara dangantakar Fulani makiyaya da manoma domin muna da shanu sama da miliyan 30 a Najeriya da za su samar mana da taki.
Yawancin Fulani makiyaya da manoman a Arewa suke, don haka bai kamata shugabannin Arewa su rika yin abubuwan da za su kawo matsala a tsakanin Fulani makiyaya da manoma ba. Muna kira ga gwamnati, kamar yadda ta ce za ta yi gandun kiwon dabbobi a Najeriya, bayan an yi wadannan gandu a giggina makarantu da asibitoci da hanyoyin mota da samar da wutar lantarki a cikinsu.
Dokokin da gwamnoni suke kafawa kuma su rika duba su da idon rahama, bai kamata su rika kafa dokoki don suna takarar siyasa ba, saboda haka rikicin Fulani makiyaya da manoma da ake yi a jihohin Taraba da Benuwai rikici ne da siyasa ke ta’azzara shi. Don haka muna rokon gwamnonin su dubi abin da zai kawo zaman lafiya, saboda zaman lafiya ya fi zama dan sarki. Yau idan babu shanu a Najeriya naman da muke ci dole ne za mu rika shigo da shi daga waje. Yanzu a kasashen duniya ana ta kukan cewa za a daina amfani da takin zamani wajen yin noma, saboda yana da illoli ga rayuwar dan Adam a koma takin juji da kashin shanu, saboda su ne suka fi amfani kuma ba su da illa. Kuma a kasashen Turai kayan amfanin gona da aka noma da takin juji ko kashin shanu ya fi daraja. Don haka bai kamata a ce za a kori Fulani makiyaya daga kasar nan ba. Idan muka kori Fulani makiyaya za mu rika sayo nama da kashin shanu daga waje, ka ga mun sake shiga matsala ke nan.
Aminiya: Me za ka ce kan gayyatar da Gwamnan Jihar Kano ya yi cewa Fulani makiyayan su dawo dajin Falgore, zai saukar da su ya samar musu da madatsun ruwa da abinci?
Farfesa Dadari: Kamar yadda na fada muna da shanu sama da miliyan 30 a Najeriya, don haka dajin Falgore ba zai iya daukar shanu miliyan 30 ba. Ya kamata Gwamnan Kano ya nuna iyakar wadanda zai iya dauka ya zaunar da su, ya samar musu da makarantu da asibitoci da kasuwa idan aka yi haka za a samu nasara.
Kuma ya kamata a kasafin kudin da ake yi a Najeriya a rika cire wa dabbobi kasonsu, kuma a tabbatar ana amfani da kudaden yadda ya kamata. A kasafin kudin Najeriya ba a bai wa noma muhimmanci, domin bai kamata a bai wa noma kashi 4 ba, ya kamata a bai wa samar da abinci muhimmanci a kasafin kudinmu.
Majalisar dinkin Duniya ta ce ya kamata kowace kasa ta bayar da kashi 10 zuwa 25 na kasafin kudinta ga aikin noma. Saboda haka tunda a Najeriya mun ce za mu bunkasa noma, kashi 4 na kasafin kudin da Shugaban kasa ya bai wa noma a bana bai yi ba. Ya kamata ’yan Majalisar Dokoki ta kasa daga Arewa su daga murya su ce Mai girma Shugaban kasa wannan kudi da aka ware ga harkokin noma ya yi kadan, a kara ya koma kamar kashi 10.
Aminiya: Yaya kake ganin tsare-tsaren bunkasa aikin gona da gwamnati ta fito da su?
Farfesa Dadari: Wannan gwamnati ta yi kira a koma gona, saboda ta lura tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare. A da kudin mai ne ake tunkaho da shi a kasar nan, yanzu farashinsa ya fadi kasa a duniya. Domin lokacin gwamnatin da ta gabata, ana sayar da gangar mai Dala 140 zuwa Dala 160, amma lokacin da wannan gwamnati ta zo farashin mai ya fadi zuwa kasa da Dala 30, yanzu ne ya fara dagawa Dala 36 zuwa 40.
A bara saboda hana shigo da shinkafa, kasar Thailand ta rufe kamfanonin sarrafa shinkafa da dama, masu gonaki sun rage gonakinsu a can. Ka ga idan muka bunkasa noma a Najeriya, leburori za su samu aikin yi, za a bude masana’antu a samu aikin yi.
Akwai matsaloli a tsare-tsaren bunkasa aikin noma da gwamnatin ta fito da su, misali shirin bayar da rance ga manoma da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito da shi, ya kamata idan za a bai wa manomi rancen a ba shi tun a watan Maris zuwa Afrilun kowace shekara, ta yadda da zarar ruwa ya sauka sai ya kama aikin gona. Amma a yanzu ana bayar da rance ga manoma ne a watan Agusta. Ya kamata Babban Bankin Najeriya ya bai wa kananan bankuna kudaden rance noma, a watan Fabarairu, bankunan kuma su yi kokari zuwa watan Maris su bai wa manoma. Kuma kada gwamnati ta yarda a ci gaba da shigo da shinkafa da masara da sauransu. Domin bincike ya nuna a bara, an noma masara a Najeriya kusan tan miliyan dubu 30. Kuma masu abincin kaji da masu cin masara a Najeriya adadin da suke bukata, ba wuce tan miliyan dubu 7 zuwa 10 ba. Muna da rarar tan miliyan dubu 20 na masarar, don haka babu hujjar shigo da masara Najeriya.