Sanya takunkumi ya fi rigakafi zama kariya daga COVID-19 – Sabon bincike

Kazalika, binciken ya ce daukar tsauraran matakai kamar dokar kulle, ba su da wani tasiri.

Sanya takunkumi ya fi rigakafi zama kariya daga COVID-19 – Sabon bincike

Wani dan Najeriya sanye da takunkumi.

Wani sabon bincike na kasa da kasa ya gano cewa yin amfani da takunkumi ne hanya mafi tasiri wajen samun kariya daga cutar COVID-19.

Binciken ya gano cewa ko da yake rigakafin cutar na taka muhimmiyar rawa wajen yaki da ita, amma ba ya bayar da tabbacin 100 bisa 100 na kariya, musamman a daidai lokacin da kasashe ke ci gaba da fafutukar yi wa mutanensu rigakafin.

Binciken, wanda masana daga Jami’ar Monash da takwararta ta Edinburgh da ke Birtaniya suka gudanar ya ce anfani da takunkumin na kare kamuwa da cutar da kaso 53 cikin 100.

Jaridar Guardian ta Birtaniya ta rawaito cewa a karon farko, an gano cewa amfani da takunkumin, bayar da tazara da kuma wanke hannu dukkansu na taka muhimmiyar rawa a yaki da cutar, amma duk takunkumin ya fi su tasiri.

A cewar masanan, binciken na nuna bukatar ci gaba da amfani da takunkumin, bayar da tazara da kuma wanke hannuwan da ma ita kanta allurar rigakafin.

Kazalika, binciken ya bayar da shawarar cewa daukar tsauraran matakai kamar na dokar kulle, rufe kan iyakoki, makarantu da masana’antu ba su da wani amfani ga al’umma, in banda illar da suke haifarwa.

A baya dai, matakai irin wadannan an yi amfani da su wajen yaki da cututtuka kamar murar tsuntsaye, kuma kasashe a fadin duniya sun yi amfani da su wajen yaki da COVID-19.

Sai dai har zuwa yanzu, masana sun kasa gano ko matakan sun yi tasirin da aka yi tsammani ko kuma a’a.

Binciken ya kuma yi la’akari da sakamakon da aka tattara daga kasashe sama da 30 na sassan duniya daban-daban, inda aka gano amfani da takunkumin na da tasirin kaso 53 cikin 100, bayar da tazara na da kaso 25 kacal, sai wanke hannu da ya nuna tasirin kaso 53 cikin 100.

To sai dai binciken bai iya auna matakai kamar irinsu killace mutane ba, dokar kulle, rufe iyakoki, makarantu da wuraren aiki saboda banbance-banbance, inji masanan.

A farkon bullar annobar dai, kasashe da dama ne suka rungumi amfani da takunkumin, amma bayan kusan shekara biyu, akasarinsu sun daina tsanantawa wajen amfani da shi.