Sanyi: Masunta sun hadu da azal a Taraba
Wani masunci ya gamu da ajalinsa sannan abokan sana’arsa su biyu na nan rai-kwakwai-mutu-kwakwai bayan da suka je su a wani tafki da ke kusa da kauyen Sarkin Kudu a karamar Hukumar Ibbi a Jihar Taraba. Yayan wadanda hadarin ya rutsa da su, Malam Haruna Yakubu ya shaida wa wakilinmu cewa, ’yan uwansa ukun sun […]
Wani masunci ya gamu da ajalinsa sannan abokan sana’arsa su biyu na nan rai-kwakwai-mutu-kwakwai bayan da suka je su a wani tafki da ke kusa da kauyen Sarkin Kudu a karamar Hukumar Ibbi a Jihar Taraba.
Yayan wadanda hadarin ya rutsa da su, Malam Haruna Yakubu ya shaida wa wakilinmu cewa, ’yan uwansa ukun sun tafi tafkin ne da misalin karfe 4:00 na dare cikin tsananin sanyi don yin su, ya ce har sun fara sun, sai sanyi ya takura musu inda suka nemi agaji daga jama’ar da ke kusa domin a fid da su daga cikin ruwan.
Ya ce kafin sauran masunta su isa inda suke sai suka kame a cikin kwale-kwalen da suke ciki su. Ya ce da aka fid da su daga kwale-kwalen sai aka kai su gefen tafkin aka hada wuta kusa da su don ceto rayukansu. “Haka ya taimaka waje farfadowar biyu daga cikinsu amma na uku mai suna Uba ya rasu,” inji shi.
Ya ce tsananin sanyin da aka fuskanta a yankinsu ya tilasta wa mutane kaurace wa su cikin dare domin gudun abin da ya faru da ’yan uwansa.
Malam Haruna ya ce har yanzu sauran mutum biyun ba su murmure ba, kuma ya ce rabon al’ummar yankin su ga irin wannan sanyi mai tsanani irin na bana ya haura fiye da shekara arba’in.