Sanyi na kawo cikas ga noman rani a Katsina

Yanayin sanyin da aka samu a ’yan kwanakin nan ya kawo cikas ga noman rani a Jihar Katsina. Kamar yadda aka saba a Kudancin jihar manoma kan yi wa tumatiri ban-ruwa a duk bayan kwana uku yayin da akan yi na dankalin Turawa duk bayan kwana biyar zuwa bakwai. Kamar yadda wadansu manoma a Funtuwa […]

Sanyi na kawo cikas ga noman rani a Katsina

Wata gonar dankalin Turawa ta rani a Katsina

Yanayin sanyin da aka samu a ’yan kwanakin nan ya kawo cikas ga noman rani a Jihar Katsina. Kamar yadda aka saba a Kudancin jihar manoma kan yi wa tumatiri ban-ruwa a duk bayan kwana uku yayin da akan yi na dankalin Turawa duk bayan kwana biyar zuwa bakwai.

Kamar yadda wadansu manoma a Funtuwa suka ce a lokacin da Aminiya ta zanta da su, sun ce ba za su yi wasa da lafiyarsu ba a wajen noman ranin ganin yadda yanayin sanyin ya tsananta.

“Mu dubi yadda ma’aunin yanayi na Celcius ya nuna daga maki 9 zuwa 13 maimakon 30 da muka saba da shi a wannan ma’auni. Hakika, gonakinmu su ne jarinmu da duk wani abin da muke tinkaho da shi; amma hakan ba zai sa mu yi wasa da lafiyarmu ba a irin wannan yanayi na sanyi kamar yadda ake ciki,” inji Malam Ja’afar Musa daya daga cikin manoman.

Ya ce, noman rani abu ne da ke bukatar kulawa musamman a wajen ban-ruwa wanda mafi yawa an fi yinsa da dare ba ma kamar inda ke da madatsar ruwa a wannan yanki.

Malam Ja’afar ya ce tilas ta sa manoman tumatir da dankalin Turawa suka kaurace wa yin ban-ruwan a makon jiya saboda yanayin sanyi.

Har ila yau, manomin ya ce, wannan kauracewar na da nasaba da kauce wa kamuwa da ciwon huhu ko ko wata cuta da ke da nasaba da sanyi, amma in komai ya daidaita, za su koma noman kamar yadda aka saba.

Shi kuwa Mu’azu Sule a Karamar Hukumar Danja wanda ya  ce ya yi kokarin zuwa gonarsa duk da sanyin da ake ciki, ya ce, akwai hadari a ce za a tsaya a yi ban-ruwan cikin dare: “Ba abu ne mai sauki ba akwai wahala, domin duk hidimominmu muna yinsu ne cikin dare saboda samun sauki. Sannan babu hayaniya da yawa a madatsar ruwan, bayan ga kayan aikin a kammale, amma ba dukkan manomi ne zai jure wa aikin cikin dare ba saboda halin yanayin sanyin,” inji shi.

Malam Ma’azu ya ce, tsofaffin manoma ne kadai wadanda suka saba da canjin yanayin kan jure wa zuwa gona safe da dare. Ya ce wani kalubale ga manoman tumatir shi ne, yadda sanyin ke lalata ’ya’yan tumatirin wanda hakan kan sa manoman cirewa da wuri.

Isa Abdullahi wani manomi ne da ke madatsar ruwa ta hanyar Jare da ke Karamar Hukumar Bakori, cewa ya yi, manoman tumatirin kan debe shi a hankali ta yadda za su dade suna cin moriyarsa, amma a lokacin sanyi ana gaggawar debewa a kai kasuwa gudun kada a bar shi ya lalace wanda hakan kan kawo faduwar farashinsa.

Malam Isa ya kara da cewa, saboda gudun wannan faduwar ya sa wadansu manoman a Kasuwar Kokami kan yanka su shanya tumatirin don ya bushe su ajiye saboda gaba.