Sanyi zai hana jiragen sama tashi a Arewacin Najeriya – NiMet
Hukumar ta ce tuni kurar ta hana jirage tashi a Nijar da Chadi.
Hukumar Harsashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadin cewa hunturun sanyin da ke tafe da kura zai hana jiragen tashi daga ranar Alhamis.
A cewar hukumar, iskar da ake fama da ita mai dauke da buji yanzu haka ta hana jirage tashi a Jamhuriyar Nijar da Chadi, kuma ta tunkaro Arewacin Najeriya.
- Talauci zai kassaramu idan aka raba Najeriya — Osinbajo
- Najeriya A Yau: Yadda Mata Manoma Za Su Tsere Wa Maza A Bauchi
“Ana sa ran wannan kurar za ta zo Arewacin Najeriya, a sakamakon haka kuma, yanayi zai disashe.
“Hakan zai shafi yawancin sassan Arewacin Najeriya, kuma zai kai ga disashe yanayi a garuruwa kamar su Maiduguri da Nguru da Potiskum da Dutse da Gombe da Yola da Bauchi da Katsina da kuma Kano.
“Akwai yiwuwar a soke sauka da tashin jirage, saboda haka akwai bukatar kamfanonin sufurin jiragen su kiyaye da wadannan ka’idojin,” inji hukumar.
NiMet ta kuma shawarci masu tuki a kan hanyoyi da su yi tukin da lura kuma cikin natsuwa saboda disashewar yanayin da za a fuskanta.
“Mutanen da ke fama da matsalar numfashi ya kamata su lura sosai, su takaita yawan fitowa waje. NiMet za ta ci gaba da lura da yanayi da kuma ankarar da jama’a a kan lokaci.”