Sa’o’i bayan ayyana neman takara a 2023, EFCC ta sake waiwayar Rochas da sabbin tuhume-tuhume
Tun a 2021 EFCC ke tuhumar tsohon Gwamnan da yin sama da fadi da dukiyar Jihar Imo lokacin da yake Gwamna.
Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zangon Kasa (EFCC), ta gabatar da sabbin tuhume-tuhume 17 a kan tsohon Gwamnan Jihar Imo kuma Sanata mai wakiltar mazabar Imo ta Yamma, Rochas Okorocha.
A tuhumar da hukumar ta gabatar a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, EFCC ta ce Rochas ya hada baki da wasu, wadanda suka hada da mambobin jam’iyyar APC, da wasu kamfanoni biyar suka saci kudi Naira biliyan 2.9 daga asusun Gwamnatin Imo.
- Badakalar kudaden Aikin Hajji: EFCC ta cafke shugaban kamfanin Medview
- Gyaran matatun mai ya lashe N100bn a 2021 – NNPC
Hukumar ta dauki wannan mataki ne sa’o’i kadan bayan da toshon gwamnan ya kaddamar da aniyarsa ta yin takarar Shugaban Kasa a babban zaben 2023.
A watan Afrilun 2021, EFCC ta kama Okorocha sannan ta tsare shi har na tsawon kwana biyu, inda ta tuhume shi kan zargin cin hanci da rashawa.
Gwamnatin Jihar ta Imo mai ci dai na zarginsa da aikata laifukan cin hanci da rashawa, almundahana da kuma yin sama da fadi da dukiyar Jihar.
Sai dai Sanata Okorocha ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.