Sa’o’inmu sun kunyata ’yan Najeriya -Shugaba Jonathan

Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya ce ire-irensa da suka shugabanci Najeriya sun kunyata ’yan kasar, inda ya kara da cewa matasa kawai ne za su kai kasar ga gaci. Shugaba Jonathan ya yi furucin ne yayin da yake kaddamar da yakin neman zabensa na shekarar 2015, wanda aka gudanar a filin wasa na Tafawa balewa […]

Sa’o’inmu sun kunyata ’yan Najeriya -Shugaba Jonathan
Sa’o’inmu sun kunyata ’yan Najeriya -Shugaba Jonathan

Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya ce ire-irensa da suka shugabanci Najeriya sun kunyata ’yan kasar, inda ya kara da cewa matasa kawai ne za su kai kasar ga gaci.

Shugaba Jonathan ya yi furucin ne yayin da yake kaddamar da yakin neman zabensa na shekarar 2015, wanda aka gudanar a filin wasa na Tafawa balewa da ke Jihar Legas a makon jiya.
Ya ce zaben shekarar 2015 zabe ne na matasa, saboda haka ko dai su zabi matashi a dama da su ko kuma su zabi wanda ba matashi ba ya yi watsi da su.
‘Sa’o’ina sun kunyata ’yan Najeriya, kuma matasa ne za su kai kasar nan inda ake so. Na kasance a nan ne don in yi magana da matasa, wadanda za su yi zabensu na farko da kuma wadanda suke tsakanin shekaru 20 zuwa 23. Gwamnatinmu ce kawai ta yi wa matasan kasar nan ayyuka masu yawa. Mun samar da tallafin karatu ga matasa, amma dole sai sun samu sakamakon mafi kyau sannan za su amfana. Mun tura su jami’o’i masu kyau a kasashen duniya don su karo ilimi, amma ’yan adawa sun ce ba mu da tsarin da muka yi wa matasa. Shin gwamnatin da ba ta da tsari ga matasa za ta yi wannan? Mun gina makarantu a sassan kasar nan wadanda suka hada da makarantun almajirai a Arewa. Ku tambayi wadanda suke yaudarar ku, me suka gina lokacin suna mulki,’ inji shi.
Jonathan ya dage a kan cewa babu yadda za a yi maganin cin hanci ta hanyar tsorata jama’a da kama su.
Ya kara da cewa gwamnatinsa tana aiki tukuru don ganin cewa ta dakatar da cin hanci da rasahawa a tsakanin al’umma.
‘Sun ce ba za mu iya maganin cin hanci ba, amma mun kama mutane da yawa a kankanin lokaci. Muna rage cin hanci kuma hukumomin da ke yaki da cin hanci za su yi wa ’yan Najeriya jawabi. Sun ce mun yi rauni ba mu da alkibla ko tsari. Na shigo tare da marigayi ’Yar’aduwa kuma shi ne ya zabi bin doka da oda, kuma na ci gaba da abin da ya fara. Duk kasar da ba ta bin doka da oda ba kasa ba ce. Saboda haka za mu ci gaba da bin doka da oda wajen yaki da cin hanci,’ inji shi.
dan takarar Gwamnan Jihar Legas karkashin jam’iyyar PDP, Jimi Agbaje ya ce jam’iyyar PDP jam’iyya ce mai cike da adalci.
Ya ce shi ya sa ’yan takarar kujerar gwamna na jam’iyyar da ke sauran jihohin duk sababbin fuskoki ne a zabe mai zuwa.
Saboda haka ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da gudanar da mulkin adalci a sauran jihohin kasar nan ba tare da nuna bambanci ba.
Jiga-jigan jam’iyyar sun yi jawabi daya bayan daya tare da kare manufofin gwamnatin shugaba Jonathan da na jam’iyyar PDP.