saqonnin waya

A kammala gasar kwallon Kabo Editan Aminiya ka ba ni dama in yi kira ga Hukumar kwallon kafa ta karamar Hukumar Kabo, don bin bahasin abin da ya sa aka kasa kammala gasar kwallo ta Kabo. Wai wasu sun ce an ki buga wasan karshen ne don Garo ba ta shiga gasar ba. To, ko […]

saqonnin waya
saqonnin waya

A kammala gasar kwallon Kabo

Editan Aminiya ka ba ni dama in yi kira ga Hukumar kwallon kafa ta karamar Hukumar Kabo, don bin bahasin abin da ya sa aka kasa kammala gasar kwallo ta Kabo. Wai wasu sun ce an ki buga wasan karshen ne don Garo ba ta shiga gasar ba. To, ko ma dai wane dalili ne kada a tauye wa mutanen Rugar Jawo da Balan da Kanye da Kwankwamawa hakkinsu. Idan aka ki buga wannan wasa na karshe (fainal), to za mu ce, an yi abin kunya. Murtala Sule a taimaka kada a yi abin kunya wajen shirya wannan gasa. Abin da ya sa na yi wannan kira kuwa, ka san dai ko matasa ba su da aikin yi, ai wasan kwallo na dan ba su kuzari da nishadi. Saboda haka dai a yi mana adalci, in ma da hali Hukumar kwallon kafa ta Jihar Kano ta shiga cikin wannan lamari. Mun gode.
Daga Sani Robinho, Kwankwamawa, Balan, Kabo da Adabo, Jihar Kano, 08133346958

ashi a hanyar Jos zuwa Jingir

A gaskiya a ’yan kwanakin nan fashi da makami ya addabe mu a kan hanyar da ta taso daga Jos zuwa Jingir, musamman daga Fuskar-Mata zuwa Jingir, inda a kullum sai an yi fashi da makami. A haka ne ma a ’yan kwanakin nan ’yan fashin bayan sun yi fashi, suka kuma sace mata biyu. Babban kiranmu ga gwamnati, shi ne, a gaskiya ya kamata a tsaurara tsaro a hanyar, domin kare mana rayuka da dokiyoyi. Da fatan gwamnati za ta gaggauta daukar mataki a kai.
Daga Salim Abubakar Imam Jingir, Shugaban kungiyar Muryar Talaka, Reshen Jihar Filato, 08067922200.
Addu’ar bin gaskiya
Salam Editan Aminiya! Tare da fatan kowa da kowa muna cikin koshin lafiya. Addu’ata a yau ita ce: “Ya  Allah Ka nuna mana gaskiya duk inda take ka ba mu ikon bin ta, Ka nuna mana karya duk inda take, Ka ba mu ikon kauce mata.”
Daga Mudassir Ibrahim Mando Jihar Kaduna 08024122559.
Shugaba Buhari ka hukunta sojoji

Gaskiya sojojin Najeriya ba ku da kwarewa wajen aiki, ga ’yan Boko Haram suna kisan ’yan kasa, kuma kuna taya su, daga tare hanya sai kisan kiyashi kamar Hitler ya dawo? Gaskiya Shugaba Buhari ka gaggauta hukunta wadannan sojoji. Domin na tabbata ko Daura suka je, suka tarar ana Sallar Juma’a haka za su yi.
Daga Mai rajin kare hakkin ’yan Adam, Hamza Ibrahim Katsina, 07030730900. [email protected]
Tsuntsun da ya ja ruwa

Abin da ya auku da ’yan Shi’a  wani al’amari ne da bai kamata ko kusa a danganta shi da addini ba, tunda malamansu suke dora su a kai, ba hanya ce mai dorewa ba. Duniya da Lahira, domin a Musulunci duk wanda ya zagi bayin Allah da ke da marataba, hakika shari’a ta tanadar masa hukunci. Don haka tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa zai doka. Yanzu mene ne ci  gaban Musulunci a nan? Ina  rokon Allah Ya nuna mana gaskiya, ya ba mu ikon bin ta.
Daga Rabi’u Agege, Shugaban kungiyar Gizago na Jihar Legas, 09093333955, 08117893939.
Addu’ar zaman lafiya

Ya Allah Ka kawo mana karshen hare-haren ta’addancin da ’yan kungiyar Boko Haram ke kai wa bayinKa da sunan jihadi a Arewacin Najeriya da ma kasashe makwabta. Domin ba haka ake jihadi a Musulunci ba.
Daga Naziru Abubakar Sabo, Gusau, 07033565999.
Ga ’jam’iyyun adawar Nijar
’Yan jam’iyyun adawar kasar Nijar ya kamata ku yi kokarin hada kanku wuri daya, kamar yadda ’yan uwanku a Najeriya suka yi wajen yin Maja, suka tada Jam’iyyar APC, wato suka hada kai wuri daya, har suka samu nasarar lashe zaben da ya gabata. Saboda haka nake ba ku shawara ya kamata ku dunkule wuri daya domin samun nasarar lashe zaben da za ku yi nan gaba kadan. A karshe ina yi muku fatan yin zabe lafiya ku gama lafiya.
Daga Haruna Muhammad Katsina. (07039205659).

APC na da matsala a Sakkwato
Don Allah Editan Aminiya, ku gaya wa Baba Buhari ya sani a Sakkwato APC na da mastala. Jama’ar da suka zo da su daga tsohowar jam’iyyata CPC,  ko mukamin jam’iyya an hana su. A kananan hukumomi 23 na Jihar Sakkwato an hana mu na komai. Don haka Shugaba Buhari yana da kwamiti daga cikin kwamitinsa, Malam Nasiru el-Rufa’i da Faruk Adamu Jigawa, domin su ne muka zo tare da su daga CPC. Kafin su zo a tambaiyi tsohon sakatarenmu, Mustafa da Baba Dauda, Ande Sakkwato, su jiya.
Daga Abubakar Harande, ( 08170823924).
A buga ‘Magana Jari Ce’ a Aminiya
Zuwa ga Edita. Bayan gaisuwa da fatan alheri ga duk ma’aikatan Aminiya. Ina rokon a taimaka a rika buga mana labaran littafin ‘Magana Jari Ce’ a jaridar Aminiya, domin buga wasu labarai daga ‘Magana Jari Ce na daya ko na biyu ko na uku zai nishadantar da mu da fatan alheri gare ku.
Daga Babalili Adamu Wushishi, 080770I33I4.
Kira ga Katsinawa
Edita, ka dubi girman Allah da Annabin Allah, ka ba ni fili in yi kira ga matasan Arewacin kasar nan da babbar murya, musamman  iyalin Dikko, Katsinawa, masu tarin albarka kan muhimmancin zaman lafiya, mu zauna lafiya da kowa, mu nemi ilimin addini da na zamani, mu guji shan kayan maye, mu koyi sana’a don tsira da mutunci, mu kiyayi maula da bara. Allah Ya ba mu dacewa.
Daga Amiru Bakori, 01068147933.
A daina belin barayin gwamnati
Ya kamata idan hukuma ta kama barayin gwamnati a daina bayar da belinsu, saboda suna da kudin da komai yawan kudin da aka sanya musu na beli za su iya biya, tunda suna da su. Idan kuwa aka ce ba batun beli, to a nan ne mutum zai dandana kudarsa.
Daga AbdulAziz Maska, Funtuwa, 07039117305.

Salam Editan Aminiya. Da fatan kana lafiya. Ina so ka ba ni dama in yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi wa Allah, ta gyara manyan hanyoyin kasar nan ko za mu samu saukin hasarar rayuka da dukiya da jikkata ba dare ba rana, musamman hanyar da ta hada Arewacin Najeriya da Jihar Legas.  Daga Yahaya MK Kajiji, 08080323435.