Saqonnin waya 01

Addu’a ga kasafin kudi Muna fatar saka hannu ga kasafin kudin 2016 da Shugaba Buhari ya yi ya zama silar kawo karshen halin kunci da al’ummar Najeriya suke ciki. Daga karshe ina rokon Allah ya sa talaka zai gani a kasa ba kamar baya da sai dai ya ji anyi kasafi, amma ba tare da […]

Saqonnin waya 01
Saqonnin waya 01

Addu’a ga kasafin kudi

Muna fatar saka hannu ga kasafin kudin 2016 da Shugaba Buhari ya yi ya zama silar kawo karshen halin kunci da al’ummar Najeriya suke ciki. Daga karshe ina rokon Allah ya sa talaka zai gani a kasa ba kamar baya da sai dai ya ji anyi kasafi, amma ba tare da gani a kasa ba.
Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999 [email protected]
 
Ziyarar Buhari Katsina

Allah ya sa ziyarar aiki da Shugaba Muhammad Buhari ya kawo a Jihar Katsina dangane da batun farfado da tattalin arzikin jihar ya sa hakan ya amfani ’yan jihar dama al’ummar Najeriya baki daya.
Daga Comrade Sanin Shaga kofar Kaura katsina 08039433111 [email protected].

Cin hanci da rashawa
Hakika yunkurin da Shugaba Buhari ke yi na magance cin hanci da rashawa a Najeriya abin a yaba ne. Muna fatan zuwansa Birtaniya domin halartar taro kan matsalar cin hanci, ta haifar mana da kwarmin ido. Domin a fili take cin hanci da rashawa suna taimakawa wajen jefa kasar cikin duhu.
Daga Mainasara  Nasarawa Funtua. [email protected] 08034208356.

Ministoci a aiwatar da kasafin 2016
Ina kira ga ministocin Najeriya, da cewa, su nuna jajircewa da kishin kasa don ganin cewa sun aiwatar da kasafin kudin 2016, da aka ware wa ma’aikatunsu yadda ya kamata. Saboda  sai ministoci sun jajirce yadda ya kamata za a iya aiwatar da ayyukan ci gaban kasa da ake so a yi wa ‘yan  Najeriya. Najeriya na bukatar abubuwa da yawa, sakamakon rashin shugabanci nagari daga gwamnatocin da suka gabata. Saboda haka ministocin Buhari ku sa himma da jajircewa, don ‘yan Najeriya suna cikin matsala. Kuma suna bukatar taimako, masamman ma ta fannin ilimi da kiwon lafiya da aikin gona da wutar lantarki da hanyoyi.  
Daga Muhammad Babangida Kiraji Gashua 08029388699.

Fatan alheri ga Shugaba Buhari
Aminiya ina so ku taimaka min da fili don na isar da sakon godiya da murna da addu’a ta alheri ga shugaban kasrmu Muhammdu Buhari wajen tafiye-tafiyen da yake yi ba don kansa yake yi ba sai don mu ’yan Najeriya.  Yana yin haka ne don dawo da martabar kasar mu a idon duniya da kuma nemo mana masu zuba hannun jari dabunkasa tattalin arzikinmu.
Mu ci gaba da yi masa addu’ar Allah ya ba shi sa’a ya kuma dawo mana da shi gida lafiya daga dukkan tafiye-tafiyen da yake yi.  Muna rokon Allah Ya ba shi kariya daga masu neman yi masa sharri.
 Daga Rabi’u Yunus Agege  Shugaban kungiyar Gizago reshen Jihar Lagos  09093333955.

Ziyarar Buhari a Landan
Assalam  Aminiya  Hausa. Allah  ya sa  ziyarar  Shugaban     Najeriya  Muhammadu  Buhari
a birnin  Landan  kan  batun  wani  taron  yaki  da  cinhanci  da kasashen duniya  za su gudanar a Birtaniya  ya sa  kwalliya  ta  biya kudin  sabulu.
Daga Alhaji Umar  4eber  Gashua 08108003333 [email protected]

’Yan kasuwa na ficewa daga Yobe
Assalam  Edita  Don  allah  Ka ba ni  dama  domin  in  bayyana wa duniya  halin  da  al’ummar  Jihar  Yobe  ke  ciki  bayan  hana  cin kasuwani  kauyuka. Na farko  kananan  ‘yan  kasuwa  na  ci gaba da ficewa  izuwa  wasu  jihohin  domin  neman  abin  sakawa  a bakin salati,  su da  iyalansu.  Muna   kira  da  babbar  murya  zuwa ga gwamnatin  tarayya  da ta  taimaka,  ta  saka  baki  domin  a sakar wa talakawan  Jihar  Yobe  kasuwani n kauyuka.  
Daga  Garba  Sabiyola Gashu’a [email protected]

Ba a taba yin kasafin kudi irin na bana ba

Salam Edita. Don Allah ka ba ni dama in bayyana ra’ayina dangane da yadda Shugaba Buhari ya saka wa kasafin kudin bana hannu. Hakika na tsaya na yi wa kasafin kallon natsuwa. Misali shi ne, kasafin kudin da ba a taba yin irin sa ba, saboda yadda Shugaba Buhari ya tsaya kai da fata wajen ganin an yi kasafin ba tare da cutar da talakawan kasa ba. Don haka muke da tunanin samun ayyuka, wadanda talakawa za su amfana. Zan iya ba da misalin yadda bangaren noma ya samu tagomashi. Hakan  ya nuna mana shugaban da gaske yake yi. A kan dawo da martabar noma da ilimi shi ma ya biyo sahu. Akwai abubuwa da dama, amma babban abin da ya ba ni sha’awa, shi ne, yadda gwamnatin ta ware makudan kudi domin tallafa wa matasa. Domin kuwa akwai alkawarin daukar matasa domin samun horon sana’a. Tabbas wannan ya nuna akwai bambance-bambance tsakanin kasafin kudin shekarun baya.
Daga Aminu Abdu Bakanoma, Sani Mainagge, Jami’in hulda da jama’a PRO Muryar talaka reshan Kano 08028505350 [email protected]

korafi ga Gwamnatin Zamfara

Don Allah Edita ina so ku ba ni dama in bayyana korafina a kan yadda wadansu mutane wadanda ba ’yan asalin Jihar Zamfara ba suke samun takardar shaidar zama ’yan jiha (INDIGINE), suna amfani da ita
wajen mamaye guraben da ake ware wa ’yan Jihar Zamfara a ma’aikatu da hukumomi daban-daban na gwamnatin tarayya. Hakika wannan babban koma baya ne ga al’ummar Jihar Zamfara, musamman yadda za ka ga wadansu daga cikin masu samun wannan takardar shaida ko kadan ba su da alaka da Jihar Zamfara, kuma galibi ba zaune suke ba a cikin jihar, suna zuwa ne kawai domin su samu wannan takardar shaida. Don haka nake kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara, da shugabannin kananan hukumomi 14 da muke da su a Jihar Zamfara, da kuma iyayen mu sarakuna da iyayen kasa, har ma da hakimai, cewa, su ji tsoron Allah su sanya kishin al’ummarsu a gaba, su tsare mutuncin jiharmu, su daina barin wadanda ba ’yan jiha ba suna samun shaidar zama ’ya’yan jiha ‘indigine.’ Nagode.
Daga Mahmud Salihu kaura-Namoda, Mataimakin Sakataren Kudi na kungiyar Muryar Talaka reshen Zamfara 07067557586 [email protected]