Saqonnin waya (4)
Ina Sanatan Zamfara ta Arewa? Assalamu alaikum gaisuwa da fatan alheri zuwa ga babban edita da sauran abokan aikin sa, sakona zuwa ga Sanatan Zamfara ta Arewa. Don Allah me ya sa ba ma ganinka a majalisa? Daga Abban Malam kauran Namoda, Jihar Zamfara 09035886971.Mun gani a kasa Zuwa ga Shugaba Buhari a gaskiya mun […]
Ina Sanatan Zamfara ta Arewa?
Assalamu alaikum gaisuwa da fatan alheri zuwa ga babban edita da sauran abokan aikin sa, sakona zuwa ga Sanatan Zamfara ta Arewa. Don Allah me ya sa ba ma ganinka a majalisa?
Daga Abban Malam kauran Namoda, Jihar Zamfara 09035886971.
Mun gani a kasa
Zuwa ga Shugaba Buhari a gaskiya mun gani a kasar harkar tsaro. Don haka mu kara da addu’a Allah Ya bai wa gwamnati ikon yin aiki tukuru wajen kare lafiyar ‘’yan Najeriya. Kuma cin hanci da rashawa ma ka da a yi sako-sako ba. Allah Ya taimaki Muhammadu Buhari.
Daga AbdulRazak Tukur, kankara, Jihar Katsina. 08061676303.
Ga Sarkin Jama’are
Salam. Edita ka mika mini sakon gaisuwa da fatan alheri ga Maimartaba Sarkin Jama’are, mai tagwayen masu.
Daga Ibrahim Khaleel Jama’are 07030775375.
Ga Aminiya da Gwamna Tambuwal
Edita don Allah ka ba ni dama in yi wa dukkan ma’aikatan jaridarmu ta Aminiya barka da sabuwar shekara. Kuma mu matasan Jihar Sakkwato muna yi wa Gwamanan mu Matawallen Sakkwato, kuma Garkuwan Lafiyar Nassarawa fatan alheri. Da fatan in Allah Ya yarda zai ci gaba da mulki a shekara ta 2019.
Daga Murtala Amwa Kanwuiri, Sakkwato North 08050332277.
Saskon sabuwar shekara ga Shugaba Buhari
Ina taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar sabuwar shekara. Allah ya taimaki gwamnatinsa da kasata.
Daga Shehu Mansur Sule Getso, Jihar Kano. 0703707900.
Shawara ga Aminiya
Yau shekara uku ba ku buga sakona ba. Don Allah ku gyara mana shafin wasanni domin don shi muke sayen jaridar.
Daga Shamsu mai kadara Kano, Mazaunin Gombe. 08033532155.
A yi wa shugaba Buhari tuni
Salam zuwa ga gidan jaridar kasata Najeriya. Don Allah ku tuna wa Buhari alkawarin tallafin Naira dubu biyar da ya yi mana.
Daga Basiru Lungu Sheka 07040939437.
Ga wadanda suka jefi Zango
Don Allah Edita ka ba ni dama in yi tsokaci kan wadanda suka jefi A. Zango a wurin taro. Saboda mu masoyansa mun san cewa dan sunnah ba ya jifar kowa. Kai kuma Yarima ka kwantar da hankalinka. Domin hassada ba yau aka fara yi maka ba. In za mu tuna baya wasu baki a Sakkwato kashe mana kai suka so yi. Ka maida komai naka ga Allah. karamin Actor ya zama Producer mawaki da kuma Darakta. In haka kuke jin haushi mun kusa yi masa rajista da’yan fim din Indiya. Sai ku mutu. Zango dai in mai shi ya so amsarsa ko daukaka abin shi. Ba mai hanawa Allah Ya shirye ku.
Daga Ishak Sani Bakori, Masoyin A.A. Zango 07030375198.
Jinjina ga Kwankwaso
Komai da lokacion sa. Jinjina ga danmusa Sanatan Kano ta tsakiya Janhali; jan aiki Rabi’u Musa Kwankwaso. Ina yi maka fatanj alheri.
Daga Nayari Abuja Najeriya 08033121619
Kukan wadanda suka lalata ilimi
Hausawa kan ce, “yau gare ka, gobe ga dan uwanka.” Gaskiya Shugaba Buhari kana da hikima da ka hana cirar kudi da katin bankunan Najeriya a kasar waje. Mafi yawan masu korafe-korafe duk dalibai ne, don bai wuce kashi 8 cikin 100 ba na ‘’yan kasuwa. Su kuwa daliban da ke karatu, wadanda suka kai kashi 92 cikin 100, ’ya’yan jagororin gwamnatin baya. Kuma kowa ya sani ko tallafin karatu (scholarship) dan talaka bai cika samu ba; tunda iyayen su sun lalata harkar ilimi a kasar nan, bayan sun kwashe komai sai suka ketare da ’ya’yan su zuwa kasar waje. Allah ne ya hambarar da su. Abin da ya rage su fara tunanin yadda za a inganta jami’o’in kasar nan domin su mayar da ’ya’yan su.
Daga Hamza Ibrahim Katsina 07030730900
Sakon sabuwar shekara
Edita ina yi maku barka da shigowa sabuwar shekara. A gaskiya rage farashin man fetur da Gwamnatin Najeriya ta yi a farkon sabuwar shekara daga 87 zuwa 85 abu ne mai kyau, sai dai ya kamata gwamnati ta dauki mataki a kan gidajen mai da ke kara farashi da kuma boye man saboda jama’a su wahala. Muna addu’ar Allah ya kara taimaka wa wannan gwamnati da duk dan kasuwar da ke sanya dan uwan sa talaka murmushi amin.
Daga Nasiru Musa Maiyama Jihar Kebbi da Yakuba Ibrahim Majidadi Saho Rame Jihar Neja. 08062206733/07055111882.