Sarah Samir:Alkalin wasa mace ta farko a Masar
A yankin Larabawa musamman a kasar Masar (Egypt) ba a san mata da yin aikin karfi ba. Hakan ta sa da yawa daga cikin kasashen yankin Larabawa matansu ba su yin wani aikin karfi, hasalima ko wasannin motsa jiki ba kasafai ake ganin matan suna yi ba. Sai dai zamani ya canza don yanzu haka […]

A yankin Larabawa musamman a kasar Masar (Egypt) ba a san mata da yin aikin karfi ba. Hakan ta sa da yawa daga cikin kasashen yankin Larabawa matansu ba su yin wani aikin karfi, hasalima ko wasannin motsa jiki ba kasafai ake ganin matan suna yi ba. Sai dai zamani ya canza don yanzu haka a Masar an fara samun matan da ke shiga harkokin wasanni musamman kwallon kafa ana damawa da su. Wannan ne dalilin da ya sa a yanzu aka samu wata mata mai suna Sarah Samir da ta zama alkalin wasa mace ta farko da ta yi wa maza alkalanci a wasan kwallon kafa a kasar. Aminiya ta ci karo da wannan bayani ne a yanar Intanet a harshen Turanci inda ta fassarawa makarantanmu kamar haka:
Hukumar kula da kwallon kafa ta Masar watau (Egyptian Football Association (EFA) ta amincewa Sarah Samir ta zama cikakkiyar alkalin wasan kwallon kafa. Hasalima a karshen makon jiya ne hukumar ta umarci Sarah ta yi alkalanci a gasar kwallon kafa na rukunin ’yan dagaji (Amateur) a bangaren maza a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Wadi Degla da kuma ta Talaea El Gaish SC wadanda suka yin kwallo a matakin ’yan kasa da shekara 17. Wannan shi ne karon farko da mace ta taba yi wa maza alkalancin kwallon kafa a tarihin Masar.
Magoya bayan kungiyoyin da kuma su kansu ’yan kwallon sun yi mamaki da suka ga Sarah ce za ta yi musu alkalanci a lokacin da suka shiga fili don fafatawa. Wannan ya ba kowa mamaki. Jim kadan bayan an kamala wasan ne sai wani gidan Talabijin mallakar gwamnati ya yi hira da ita, inda Sarah ta nuna ba ta fuskanci wata matsala ba a lokacin da ta yi alkalancin. Hasalima ta ce tana fatan wannan zai zama somin-tabi a cigaba da aikinta na yin alkalanci.
Har ila yau a wata hira da ta sake yi da kafar sadarwar Ahram, Sarah Samir ta yi fatan za a samu mata masu yawa da za su shiga harkar yin alkalanci a wasannin kwallon kafa a kasar. Ta ce maza ’yan kwallo kan shiga taitayinsu idan suka ga mace ce take yi musu alkalanci, don sun fi amincewa a kan alkalancin mace fiye da namiji. Dalilin haka inji ta bai wuce cewa mace ta fi nuna adalci fiye da namiji a duk lokacin da ake yin alkalancin wasa ba. “Da wuya ga ji wata hatsaniya ta tashi a duk lokacin da mace ta hura wasa, ba kamar yadda maza ke yi ba”.
Ta ce alal misali akwai lokacin da aka taba gudanar da wani wasan kwallon kafa rukunin ’yan dagaji inda wani namiji ya hura, amma abin mamaki magoya bayan kungiyoyin biyu sun rika zaginsa wasu ma har da jifa suna yi masa ihu saboda ba su gamsu da yadda ya hura wasan ba, amma bayan Hukumar kwallon kafa ta Masar ta umarci a sake wasan sai aka umarce ni da in yi alkalanci a wasan karo na biyu. Abin mamaki shi ne yadda na hura wasan ba tare da wata matsala ba, hasalima kowa ya gamsu kuma na ji dadi sosai kuma ya karfafa mini gwiwa. “Na samu sakonni masu yawa na nuna farin ciki da kuma fatan alheri bayan an tashi wasan da hakan ya nuna an gamsu da ni”.
“Ganin yadda muke cikin yankin da ba kasafai ake son cakuduwa a tsakanin maza da mata ba a kowane irin sha’ani ta sa yankin Larabawa ya zama koma-baya a bangaren wasanni, musamman ma a kwallon kafa, amma yanzu da yake abubuwa sun canza, mahukunta a Masar sun fara gane muhimmancin sakar wa mata mara ana damawa da su a bangaren wasanni”.
Sarah ta kara da cewa iyalanta, watau mahaifiyarta da mahaifinta sun amince mata a kan ta cigaba da yin alkalancin kwallon kafa haka kuma ta nuna yadda jama’a da dama suke aika mata sakon fatan alheri a kan wannan harkar da ta tsunduma a ciki. Don haka ta sha alwashin sai ta ga abin da zai ture wa buzu nadi.
Sarah ta ce yanzu babban burinta shi ne ta ga ta fara yin alkalanci a gasar rukuni-rukuni na maza ajin kwararru (Professional) na kasar. Ta ce tana fata wata rana ta yi alkalanci a gasar cin kofin duniya kamar yadda shahararren alkalin wasa na kasar Essam Abdel-Fattah ya yi alkalanci a gasar cin kofin duniya a shekarar 2006. “Ina so na yi alkalanci a gasar cin kofin duniya, kasancewata matashiya mai jini a jiki, inda da yakinin zan iya cimma wannan buri.
Ita dai Sarah ta fara yin alkalanci ne a shekarar 2007 amma har yanzu ba ta fara yin alkalanci a matakin manya ba sai a rukunin ’yan dagaji da kuma wasannin da matasa ke shirya wa a unguwanni.
A wata hira da ta sake yi da gidan talabijin na CBC Channel da ke Masar ta nuna jin dadinta musamman ganin yadda jama’a da dama suka nuna gamsuwarsu a kan alkalancin da take yi, Ta ce tana fata nan gaba za a samu mata masu yawa da za su rungumi harkar alkalanci a Masar, inda za su yi kafada da kafada da maza.
A wasan da Sarah ta hura a tsakanin kulob din Wadi Degla da Taaea El Gaish a karshen makon jiya, daya daga cikin alkalan wasan da suka taimaka mata mace ce da hakan ya nuna an fara samun yawaitar mata masu yin alkalanci a kasar.
Kawo yanzu an samu mata bakwai da suka zama alkalan wasa a Masar sai dai biyar daga ciki sun kasance masu taimakawa alkalin wasa (lineswomen) ne yayin da biyu suka kasance alkalan wasa (referee) inda Sarah Samir ta kasance ta farko.