Sarakauna ba su bukatar a sanya su cikin tsarin mulki – Lamidon Adamawa
Lamidon Adamawa Alhaji Barkindo Mustafa ya ce sarakunan kasar nan ba su bukatar a sanyasu cikin kundin tsarin mulki, tunda tun farko suna ciki siyasa ce ta fitar da su don haka ba su bukatar komawa ciki don kada siyasa ta shiga cikin harkokin sarauta gara a kyale su, su kare martabar gidajensu. Lamido ya […]
Lamidon Adamawa Alhaji Barkindo Mustafa ya ce sarakunan kasar nan ba su bukatar a sanyasu cikin kundin tsarin mulki, tunda tun farko suna ciki siyasa ce ta fitar da su don haka ba su bukatar komawa ciki don kada siyasa ta shiga cikin harkokin sarauta gara a kyale su, su kare martabar gidajensu.
Lamido ya bayyana haka ne a wurin taron sarakuna karo na shida da aka yi a Sakkwato a ranar Talatar da ta gabata.
Mai martaba Lamidon ya kara da cewa, “Mu abin da kawai muke so a yi mana aba mu kariya ta mulki, gwamnatocin jihohi su daina katsalanda cikin harkokin masarautu da za ta ba su damar cire sarki a lokacin da suka ga dama, rashin kariyar mulki ita ce damuwarmu ba wai shiga cikin kundin tsarin mulki ba.”
Tun farko Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce makasudin taron da cewa shi ne domin tattauna hanyoyin kula da harkokin zamantakewa da sha’anin tsaro a kasar nan.
Shugaban kasa ta hannun Mataimakinsa Alhaji Namadi Sambo ya bayyana sarakuna a matsayin masu kare rayuwa da rugujewar kasar nan.
Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal shi ma a tofa albarkacin bakinsa ya ce “Dukkanmu mun hadu a nan ne bisa manufa daya wato ciyar da kasar nan gaba.”
Ya ce su da aka zaba a mukaman mulki, yana da kyau a taimake su a tunatar da su kan abin da za su yi ko bayan sun wuce a rika ce sun kawo wa kasa ci gaba.
Waziri Tambuwal ya ce su a majalisa suna alfahari da sarakunan gargajiya, “Shi ya sa muke son mu ba su matsayi a cikin kuindin tsarin mulki a gyaran tsarin mulki da muke yi don mun san su masu muhimmanci ne ga kasar kuma bai kamata a rika barinsu a baya ba,” inji shi.
Sauran wadanda suka yi jawabi sun hada da mai masaukin baki Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Wamakko da takwaransa na Jihar Benuwai Gabriel Suswam wanda ya yi jawabi a madadin sauran gwamnonin da suka je bikin. Sauran gwamnonin da suka halarci taron sun hada da na jihohin Gombe da Kaduna da Kebbi da Bauchi.