Saraki ga Buhari: Ana jin jiki a Najeriya
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki ya shaida wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ana jin jiki a Najeriya kuma ’yan Najeriya suna fama da wahala. Sanata Bukola Saraki ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba lokacin da yake magana lokacin da Shugaba Buhari yake gabatar da kasafin kudin badi , inda Saraki ya koka […]

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki ya shaida wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ana jin jiki a Najeriya kuma ’yan Najeriya suna fama da wahala.
Sanata Bukola Saraki ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba lokacin da yake magana lokacin da Shugaba Buhari yake gabatar da kasafin kudin badi , inda Saraki ya koka kan yadda ake jin jiki a kasar nan.
“Mai girma Shugaban kasa, abin da mutane suke shaida mana a duk lokacin da muka ziyarci mazabunmu daban-daban shi ne ana jin jiki a kasar nan. Muna ganin hakan, kuma muna ji a jikinmu. Wannan hali da ake ciki yana bukatar mu mike dukkanmu a matsayinmu na gwamnati don daukar matakan gaggawa. Ba dabo za mu yi ba, amma wajibi ne mu yi aiki wurjanjan.”
Ya kara da cewa: “Wajibi ne mutanenmu su ga wani yunkuri daga gwamnati na nemo mafita daga kuncin tattalin arziki da ake ciki; kuma wajibi ne a sadaukar da kai wajen saukaka wahalar da suke sha. Ba su bukatar sanin wace jam’iyyar siyasa muka fito, ko wane harshe muke magana da shi ko yadda muke bauta wa Allah. Sun mika amanarsu a hannunmu kuma suna bukatar mu kara kokari fiye da baya don sauke nauyin da suka dora mana.”
Shi ma da yake gabatar da jawabin godiya Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya ce wajibi ne Shugaba Buhari ya sanya ayyukan da aka yi watsi da su da manyan ayyuka a jerin manyan abubuwan da zai magance.
Ya ce, “Ku taya ni kira da Shugaban kasa ya kara sauya fasalin kasafi ta sanya manyan ayyukan da aka yi watsi da su da manyan ayyuka a cikin jerin abin da zai kashe baya ga cin hanci da rashawa.
Dogara ya ce ana samun matsala ne a kasafin kudin shekara-shekara ne saboda ba a cika cimma manufofin da aka tsara ba.
Shi ma a yayin da yake gabatar da kasafin Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kusan daukacin al’ummar kasar na jin radadin koma bayan tattalin arzikin da kasar ke ciki a yanzu.
Sai dai ya ce an tsara kasafin kudin na Naira tiriliyan bakwai da biliyan 300 ne ta yadda zai tsamo kasar nan daga cikin halin da ta shiga.
Shugaba Buhari ya ce za a kashe Naira tiriliyan 7 da biliyan 298 a badi, wato karin fiye da kashi 20 a kan kasafin kudin bana.
Ya ce za a kashe kashi 30 cikin 100 na kasafin kudin domin gudanar da manyan ayyuka, kuma kasafin kudin zai bayar da muhimmanci wajen farfado da masaku a Aba da Anicha da Kaduna da Kano da Nnewi da kuma Otta.
A cewarsa, za a yi amfani da kudin da ake samu ta hanyar man fetur wajen inganta harkar noma, kuma gwamnatinsa za ta samar da ayyukan yi ga matasa.
Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin ne bayan da Majalisar Zartarwa ta kasa ta amince da gabatar da daftarin kasafin kudin a zaman da ta yi ranar 30 ga watan Nuwamba.
An bana an yi fama da jerin badakalar yin coge a tsakanin ’yan Majalisar Dokokin ta kasa a kasafin kudin 2016.