Saraki ya bukaci Oshiomhole ya fice daga harkokin siyasa
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki ya ce, sakamakon binciken da ake yi shugaban jam’iyyar APC na Kwamred Adams Oshiomhole bai da wani gurbi da zai sa ya ci gaba da zama don gudanar da harkokin siyasa. Wannan tuhumar zargin da ake yi wa Oshiomhole nada alaka da cewa, ya karbi wasu abubuwa daga hannun […]
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki ya ce, sakamakon binciken da ake yi shugaban jam’iyyar APC na Kwamred Adams Oshiomhole bai da wani gurbi da zai sa ya ci gaba da zama don gudanar da harkokin siyasa.
Wannan tuhumar zargin da ake yi wa Oshiomhole nada alaka da cewa, ya karbi wasu abubuwa daga hannun ‘yan takara lokacin zaben fidda gwani, wanda ya yi sanadiyya sanya jam’iyyar a cikin rikici.
Saraki ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a wajen addu’ar cika shekara shida da rasuwar mahaifin Saraki, Dakta Olusola Saraki, inda shugaban majalisar ya ce, a yanzu Oshiomhole bai da abin zai iya fada game da siyasar Najeriya.