Saraki ya rantsar da sabbin Sanatoci, Kaita da Gumau
Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a yau Laraba ya rantsar da Sanata Ahmed Babba Kaita da Sanata Lawal Yahaya Gumau wadanda suka maye gurbin Sanatocin da suka rasu. Sanata Ahmed Babba Kaita daga mazabar Katsina ta Arewa wanda ya maye gurbin marigayi Mustapha Bukar yayin da Sanata Lawal Yahaya Gumau ya maye gurbin Malam Ali […]
Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a yau Laraba ya rantsar da Sanata Ahmed Babba Kaita da Sanata Lawal Yahaya Gumau wadanda suka maye gurbin Sanatocin da suka rasu.
Sanata Ahmed Babba Kaita daga mazabar Katsina ta Arewa wanda ya maye gurbin marigayi Mustapha Bukar yayin da Sanata Lawal Yahaya Gumau ya maye gurbin Malam Ali Wakili daga mazabar Bauchi ta kudu wanda ya rasu kwanaki.
Saraki ya taya Sanatocin murnar shigowar majalisar a matsayin abokanan aiki.