Saraki ya sake shan kaye a kotu

Kotun da’ar Ma’aikata (CCT) da ke Abuja, ta ce tana da ikon yi wa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki shari’a kan zarginsa da ake yi masa na cin hanci da rashawa.A zaman kotun na jiya Alhamis Shugaban Kotun Mai shari’a danladi Umar ya yi watsi da bukatar da Sanata Saraki ya gabatar ta hannun […]

Saraki ya sake shan kaye a kotu
Saraki ya sake shan kaye a kotu

Kotun da’ar Ma’aikata (CCT) da ke Abuja, ta ce tana da ikon yi wa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki shari’a kan zarginsa da ake yi masa na cin hanci da rashawa.
A zaman kotun na jiya Alhamis Shugaban Kotun Mai shari’a danladi Umar ya yi watsi da bukatar da Sanata Saraki ya gabatar ta hannun lauyansa yana kalubalantar ikon kotun na yi masa shari’a.
Sanata Saraki ta hannun lauyansa, Kanu Agabi (SAN) ya gabatar da wata bukata yana neman a yi watsi da zarge-zargen cin hanci da ake yi masa. Kuma a kalubalantar ikon kotun ya kawo wasu batutuwa da Kotun koli ta riga ta yanke shawara a kai.
Lauyan kariyar ya ce, gazawar Hukumar Kula da da’ar Ma’aikata (CCB) na ta gayyaci Sanata Saraki don sanar da shi inda ya keta doka tare da rashin bin ka’ida wajen cika fom din bayyana kadarorinsa ya kawo nakasu ga halaccin tuhumce-tuhumcen da ake yi masa, don haka sai ya soki matakin na hukumar na zuwa kotun.
Sai dai lauya mai gabatar da kara, Rotimi Jacobs ya yi fatali da wannan bayani, inda ya bayyana shi da marar tabbas kuma shiririta da wasa da kuma raina kotu. Don haka sai Mista Jacobs ya bukaci kotun da ta yi fatali da wannan bukata.
Lokacin da yake yanke shawarar watsi da bukatar alkalin kotun Mai shari’a danladi Umar ya ce shari’ar tana karkashin ikon kotun na ta saurara, don haka ya bayyana cewa a shirye kotun take ta ci gaba da sauraren shari’ar.
A jiya lauyoyi 80 ne suka yi rakiya wa Sanata Saraki ciki har da manyan lauyoyi (SAN) guda 10 domin ba shi kariya a yayin shari’ar.
Alkalin kotun ya ajiye ranar 5 ga Afrilu mai zuwa domin fara sauraren shari’ar gadan-gadan.