Saraki ya taya Atiku murnar lashe zaben fitar da gwanin PDP
Ya kuma jinjina wa magoya bayansa kan gudunmawar da suka ba shi
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma daya daga cikin wadanda suka nemi takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP, Bukola Saraki, ya taya dan takarar jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar murnar lashe zaben fid da gwanin jam’iyyar.
A ranar Asabar ce dai Atiku ya lashe ya zama dan takarar PDP a zaben 2023 mai zuwa bayan ya kayar da su Sarakin da sauran ’yan takara, yayin zaben da aka gudanar a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja.
- Atiku ya lashe zaben dan takarar shugaban kasar PDP
- Atiku: Karo 6 a shekara 30 na neman kujerar shugaban kasa
- 2023: Ina nan ina jiranka mu fafata — Tinubu ga Atiku
Saraki ya kuma gode wa dukkan abokansa da magoya bayansa a fadin kasar nan kan yadda suka ba da himma wajen samar da manufarsa ta kawo sauyi da ake kira: #RealSolutions da #FixNigeria!
Ya kara da cewa, “Yayin da muke shirin tunkarar babban zaben gaba, ina alfahari da cewa sakonmu na #RealSolutions da jagoranci na gari ya ratsa zukatan miliyoyin matasan Najeriya a fadin kasar nan.
“Yanzu, dole ne mu hada kan dukkan ’yan takararmu a fadin kasar nan don gyara tattalin arzikinmu, mu dakile matsalar rashin tsaro da kuma kawo karshen tsadar rayuwa,” inji shi.
Bukola Saraki ne dai ya zo na uku a zaben da kuri’a 70 a zaben fid da gwani na Shugaban Kasa na jam’iyyar, wanda ’yan takara 14 suka fafata a cikinsa.