Sarakuna Arewa ga Jonathan: Kashe-kashen sun isa haka nan
Sarakunan Arewa sun bukaci Shugaba Goodluck Jonathan ya dauki kwakkwaran mataki kan kashe-kashen da ake yi a Arewa, inda suka bayyana cewa kashe-kashen da ake yi a yankin sun isa haka nan. Sun bukaci hakan ne a lokacin da suka yi taron gaggawa a dakin taro na Lugard Hall da ke Kaduna shekaranjiya Laraba. Sarakunan […]
????????????????????????????????????

Sarakunan Arewa sun bukaci Shugaba Goodluck Jonathan ya dauki kwakkwaran mataki kan kashe-kashen da ake yi a Arewa, inda suka bayyana cewa kashe-kashen da ake yi a yankin sun isa haka nan.
Sun bukaci hakan ne a lokacin da suka yi taron gaggawa a dakin taro na Lugard Hall da ke Kaduna shekaranjiya Laraba.
Sarakunan sun nuna matukar damuwarsu kan kashe-kashen da ake yi a Arewacin Najeriya da kuma ci bayan da yankin yake samu, inda suka bukaci Shugaban kasa ya dauki matakin gaggawa don kawo karshen kashe-kashen jama’a da ake yi a yankin.
A lokacin da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad yake jawabin bude taro a matsayinsa na Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa ne ya ce kashe-kashen da ake yi a Arewa musamman ma Arewa maso Gabas na matukar damunsu, don haka “ba za mu yi shiru mu zuba idanu ba, saboda al’ummarmu ake kashewa kowace rana.”
“Jama’a suna ganinmu a matsayin iyayen kasa, don haka a matsayinmu na iyaye ya sa muka gudanar da wannan taro don mu nuna rashin jin dadinmu dangane da rashin tsaro a Arewa wanda ya haifar da asarar rayuka da kuma dukiya. Don haka muna mika kukanmu ga Shugaban kasa don ya dauki matakin gaggawa a kan al’amarin, kasancewar ba za mu yi shiru har matsalar ta cinye mu ba.”
Ya ce jama’ar da suke wannan dakin taron su ne shugabannin majalisar sarakuna a jihohin Arewa, sun kuma yi tarurruka da ’yan majalisarsu da suka hada da dagatai da hakimai kafin suka halarci wannan taron. Yanzu muna magana da murya daya da kira ga Shugaba Goodluck Jonathan cewa kasha-kashen sun isa haka.
“Kowa a kasar nan yana da masaniyar abin da yake faruwa a Arewa, musamman Arewa maso Gabas, musamman ma shekaru biyu da suka gabata, ba za a ci gaba da kasancewa haka ba. Muna kira ga shugaban kasar da Allah Ya dora mana don ya ja ragamar kasar nan da ya saurari koke-koken da al’umma ke yi, saboda abin da yake faruwa a kasar nan zai haifar da cikas ga bunkasar da kuma hadin kan yankin Arewa, wanda hakan zai shafi kasa gaba daya. Don haka ya zama tilas a kawo karshen matsalar rashin tsaro a yankin.” Inji Sarkin Musulmi.
Majalisar Sarakunan ta yi wannan taron ne kwanaki biyu bayan ’yan Boko Haram sun nada sarakuna a Gwoza da Danbowa a Jihar Barno.
Sarakunan da suka halarci taron sun hada da Shehun Barno, Alhaji Garbai Ibn El-Kanemi da Sarkin Kano Muhammad Sanusi na III da Etsu Nupe, Yahaya Abubakar da Gbong Gwom na Jos, Jacob Buba Gyang da Attah na Igala, Idakwo Ameoboni na II da kuma Sarkin Zazzau, Dokta Shehu Idris.