Sarakuna su kafa kwamitocin sulhunta manoma da makiyaya – Dan Ali
Shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa reshen Jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu dan Ali ya nemi sarakunan kasar nan da su rika kafa kwamitoci da za su kawo karshen rashin jituwa da take tasowa a tsakanin al’ummar Fulani makiyaya da manoma, kamar yadda masarautar Argungu ta yi a kwanakin baya. Alhaji Muhammadu dan Ali ya bayyana […]
Shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa reshen Jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu dan Ali ya nemi sarakunan kasar nan da su rika kafa kwamitoci da za su kawo karshen rashin jituwa da take tasowa a tsakanin al’ummar Fulani makiyaya da manoma, kamar yadda masarautar Argungu ta yi a kwanakin baya. Alhaji Muhammadu dan Ali ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Birnin Kebbi.
Shugaban kungiyar ya cigaba da cewa, ta hanyar da masarautar Argungu tabi ta kafa kwamitici domin gano matsalolin dake faruwa tsakanin Fulani makiyaya da manoma ce mafita, domin asan hanyoyin da za a magance su acikin ruwan sanyi. Alhaji Muhammadu Dan Ali ya ce idan ana son irin wadannan kwamitocin su yi tasiri, to ya kamata a kafa su a kowace masarauta a kasar nan ya ce idan aka yi haka za a sami hanyar da za a magance matsalar.
Ya yi amfani da wannan dama, inda ya yi kira ga sarakunan kasar nan da hakimansu da su ci gaba da ba Fulani makiyaya goyon baya da kuma ba su hakkin su kamar yadda suke ba manoma domin su ma talakawansu ne kamar yadda manoma suke a gare su.
Shugaban ya ce, rashin adalci da Fulani ke samu daga dukkan hukumomin gwamnati shi ne babban dalilin da yasa aka raina fulanin kuma a kowane lokaci ake maida su baya tamkar ba ‘yan kasa ba. Ya ce a kasar nan duk da cewa Fulani na bada kaso mai tsoka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa kamar samar da nono da madara da fatu da kirgi da nama da kuma biyan haraji, makiyaya ne kawai suke rasa kaso cikin kasafin kudi na tarayya jihohi da kananan hukumomi.
Shugaban ya ce da zaka ji cewa an tanada a ma’aikatar gona, a karshe manoma ne ake baiwa ba wani abu na makiyayi alhali su manoman kuma a karshe sune za a je a hada su fada da makiyayan, manyan hanyoyin kasar nan an ginasu ne akan labin shanu, amma ba wadansu sabbin hanyoyin shanu da ake fitar wa Fulani, don haka mutum ne ka tare masa hanya ka tare masa wajen shan ruwa kuma ka ce ya zauna waje guda, ta ina zai zauna?, dole sai gwamnatoci sun yi musu adalci kafin su zauna waje guda.
Da karshe ya yi kira da Fulani makiyaya da su kauce wa shiga gonakin manoma domin kawo zaman lafiya da cigaban kasa, su kuma rika bin doka da oda da girmama sarakuna a duk inda su ke.