Sarakunan Arewa sun koka da halin da ’yan gudun hijira ke ciki
Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa kuma Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa’ad Abubakar ya koka da halin kunci da ’yan gudun hijira ke ciki a yakin Arewa, musamman yankin Arewa maso gabas, mai fama da rikicin Boko Haram; inda ya kalubalanci gwamnonin Arewa da su tabbatar da sun gano inda biliyoyin kudin da aka tara domin tallafa […]
Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa kuma Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa’ad Abubakar ya koka da halin kunci da ’yan gudun hijira ke ciki a yakin Arewa, musamman yankin Arewa maso gabas, mai fama da rikicin Boko Haram; inda ya kalubalanci gwamnonin Arewa da su tabbatar da sun gano inda biliyoyin kudin da aka tara domin tallafa wa ’yan gudun hijirar.
A cewarsa, akwai bukatar a gano inda wadannan kudade suke, domin a taimaka wa ’yan gudun hijirar da su, domin manufar tara kudin ke nan.
Sultan ya yi wannan furuci ne a wajen taron sarakunan Arewa da aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata a Jihar Kaduna. Ya ce kudin an tara su ne saboda inganta jin dadin ’yan gudun hijirar amma a yanzu irin labaran da ake yadawa a kafafen watsa labarai, abin bakin ciki ne.
“Saboda haka akwai muhimmanci sosai a tabbatar da an raba wadannan kudade ta hannun gwamnoni. A duk lokacin da muka hadu da shugabanninmu na siyasa, mukan fada masu gaskiya kuma abin da muke yi ke nan a nan kuma za mu ci gaba da shawartarsu a duk lokacin da bukatar hakan yta taso.
“Za mu ci gaba da shawartarsu domin jin dadi da ci gaban al’ummarmu, musamman a yankin Arewa. Mun tabbatar da cewa idan har aka kawo karshen matsalolin Arewa, muna da yakinin Najeriya za ta zauna lafiya. Saboda haka ne za mu tattauna matsalolin Arewa da Najeriya baki daya.”
Ya ci gaba da cewa: “Za mu tattauna matsalolin ’yan gudun hijira a yankin Arewa maso gabas. Mutanen na cikin wahala kuma biliyoyin nairori aka amsa ko kuma aka ware domin kulawa da ’yan gudun hijira amma abin da muke ji a kafafen watsa labarai babu dadin ji.
“Saboda haka ya dace a raba wadannan kudade domin jin dadin ’yan gudun hijirar nan. Dole ne a yi amfani da kudaden saboda idan mutum ya rigaya ya mutu ba ya bukatar wani abu sai addu’a. saboda haka tun da ’yan gudun hijirar na raye, sai mu taimaka masu. Dole mu kula da su saboda ’yan uwanmu ne maza da mata. Muna rokon gwamnonin da su dauki batun da muhimmanci; ta hanyar sanar da Shugaban kasa, domin a saki kudade, domin ina cikin wadanda suka halarci taron da aka yi domin tara kudin a waccen gwamnati saboda kulawa da ’yan gudun hijira.
Sultan din ya kuma nuna damuwarsa game da ikirarin da matasan MASOB ke yi na neman kasar Biyafara, inda ya ce akwai ’yan kabilar Igbo da ke zaune a Arewa masu yawan gaske kuma a nan suke sana’oinsu, domin ba su da inda za su tafi saboda haka sai ya ce majalisar sarakunan za ta kafa kwamiti da zai ziyarci can yankin na Kudu domin ganawa da sarakunansu a kan wannan batu.
Shi kuwa Gwamnar Jihar Adamawa, Jibrila Bindow kira ya yi ga sarakunan da su taimaka wajen hana ’yan gudun hijira na bogi yin tururuwa zuwa cikin sansanonin ’yan gudun hijira da ke kasar nan.