Sarakunan Arewacin Gombe sun bukaci jama’a su zauna lafiya

Sarakunan Nafada da Funakaye da Hakimin Kwami da ke Arewacin Jihar Gombe sun bukaci al’ummar yankin su zauna lafiya, inda suka ce sai da zaman lafiya za a samu ci gaban kasa.Sarakunan sun bayyana haka ne a lokacin da suke karbar shugabanin kungiyar ci gaban yankin Gombe ta Arewa a masarautunsu.Sarakunan Alhaji Muhammadu Dadum Hamza […]

Sarakunan Arewacin Gombe sun bukaci jama’a su zauna lafiya
Sarakunan Arewacin Gombe sun bukaci jama’a su zauna lafiya

Sarakunan Nafada da Funakaye da Hakimin Kwami da ke Arewacin Jihar Gombe sun bukaci al’ummar yankin su zauna lafiya, inda suka ce sai da zaman lafiya za a samu ci gaban kasa.
Sarakunan sun bayyana haka ne a lokacin da suke karbar shugabanin kungiyar ci gaban yankin Gombe ta Arewa a masarautunsu.
Sarakunan Alhaji Muhammadu Dadum Hamza da Alhaji Abubakar Kwairanga da Alhaji Haruna Abdullahi sun tabbatar da goyon bayansu don ganin komai ya gudana yadda ya kamata a yankin, inda suka ce yankin Gombe ta Arewa ne yankin da ya fi yawan jama’a a jihar amma an bar shi a baya an fannin ayyukan raya kasa.
Iyayen kasar sun yi kira ga gwamnatocin a dukkan matakai su samar wa manoma takin zamani don bunkasa noma a daminar bana.
Tunda farko a jawaban Shugaba da Sakataren kungiyar Alhaji Salisu Sheriff da Sa’idu Gimba Tafida sun shaida wa iyayen kasar cewa sun zo fadojinsu ne domin bayyana jin dadinsu kan yadda suke samar da kyakkyawan hadin kai don ciyar da yankin gaba. Sun ce kungiyar tana yin duk mai yiwuwa domin rage zaman banza a tsakanin matasa.
Dattawan kungiyar, Alhaji Umaru Gurama da Alhaji Yaya Hammari da Hajiya Hauwa Bajoga, sun ce siyasa ba za ta hana su yin duk abin da ya dace ba, don haka su shaida wa al’umma manufar kungiyar don ganin an kafa rassanta a kananan hukumomin yankin.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe