Sarakunan Fulani a Kudu sun kuduri aniyar samar da tsaro a kasa
Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihohi 17 na Kudu, Sardaunan Yamma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin, ya ce taron da Sarakunan Fulani na wannan sashe suka yi a Asabar da ta gabata, a karkashin jagorancinsa ya tattauna ne a kan muhimman abubuwa uku da suka danganci irin goyon bayan da Fulani za su bayar ga […]
Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihohi 17 na Kudu, Sardaunan Yamma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin, ya ce taron da Sarakunan Fulani na wannan sashe suka yi a Asabar da ta gabata, a karkashin jagorancinsa ya tattauna ne a kan muhimman abubuwa uku da suka danganci irin goyon bayan da Fulani za su bayar ga tsaron kasa.
“Na farko, taron ya amince cewa daga yanzu Sarakunan Fulani da ke zaune a wannan sashe za su fara aiki da shawarar Shugaba Muhammadu Buhari a kan batun tantace baki da ke ziyarar garuruwa da rugagensu, domin guje wa karbar bakuncin miyagun mutane masu barazana ga tsaron lafiyar Najeriya. Na biyu kuma mun tattauna ne a kan irin gudunmawar da za mu bayar ga shirin murkushe barayin shanu da gwamnatocin jihohin Arewa suke yi. Abu na uku shi ne matsalar da ta-ki-ci-ta-ki-cinyewa a tsakanin manoma da makiyaya.”
Da yake yi wa ’yan jarida bayani bayan kammala taron kwana daya a fadarsa, Maiyasin ya ce: “Daga yanzu sarakuna da shugabannin Fulani za su fara aikin binciken kwakwaf ga dukkan mutumin da ya ziyarci rugarsu domin neman zama tare da su saboda guje wa karbar miyagun mutane masu barazana ga tsaron lafiya. Kuma za mu kafa kwamitocin hadin gwiwa a tsakaninmu da dillalan shanu domin gano shanun da aka sato daga wasu wurare da za mu kwace mu mika su ga jami’an tsaro.
Sannan kuma za mu bi diddigin gano irin laifin makiyaya da manoma suke yawan korafi a kan cinye masu amfanin gona da dabbobi suka yi a wannan sashe. Dukkan Bafulatanin da muka same shi da laifi a kan wannan matsala, za mu tabbatar da cewa ya biya diyya ga manoma idan ya ki mu mika shi ga ’yan sanda.”
Ya ce wannan babban aiki ne kuma nauyi ne a wuyansu da ya kamata su tashi tsaye su wayar da kan jama’arsu a game da yin kyakkyawar lura da irin mutanen da suke zaune tare da su a cikin unguwanni da garuruwa. Ya nemi sarakunan Hausawa na sashen Kudu da su yi koyi da wannan mataki wajen yin binciken irin mutanen da suke tasowa daga sashen Arewa, suna shigowa cikinsu da sunan cirani amma da mummunan nufi a zukatansu. Irin gudunmawar da ya kamata su bayar ke nan ga fafutukar samar da zama lafiya da tabbatar da tsaro da Shugaba Buhari yake yi a kasar nan.