Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi 

Sarkin ya ce sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni face suna mutunta kansu ne da kuma gudun magana.

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi 

Sarkin Musulumi Muhammad Sa’ad Abubakar

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya musanta maganar da ke cewa sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnonin jihohi.

Ya bayyana cewa sarakunan gargajiya sun daɗe suna mulki tun kafin samun ’yancin kai a Najeriya, kuma suna da cikakkiyar fahimta game da ƙasa sama da gwamnonin jihohi.

Sarkin ya yi wannan bayani ne a taron tattaunawa kan cigaban matasan Arewacin Najeriya, wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya a Abuja ranar Talata.

Ya mayar da martani ne, game da kalaman tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, wanda ya ce sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnoni.

Sarkin Musulmi ya ce, “Na ji wasu suna cewa sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnonin jihohi. Wannan ba gaskiya ba ne.

“Sarakunan gargajiya kawai suna mutunta kansu ne da kuma mutunta gwamnonin, waɗanda ke da iko a jihohinsu. Ba wai tsoro ba ne.

“Idan wani abu ya faru, muna barinsa ga Allah Mai iko a kan komai. Muna karɓar duk wani sauyi da ya zo.

“Kafin a samu gwamnonin jihohi, sarakunan gargajiya sun riga sun fara mulki a wuraren da suka zama Najeriya tun daga 1914, kafin samun ’yancin kai a 1960.

“A matsayinmu na shugabannin gargajiya, muna da kusanci sosai da al’ummarmu saboda mun san buƙatunsu, kuma muna tare da su duk lokacin da wani abu ya faru.”