Sarakunan Hausawa biyu a Ibadan sun tuɓe rawanin juna

Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Ɗahiru Zungeru ne ya fara sanar da cewa ya tuɓe rawanin Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin a wajen taro da ’yan jarida

Sarakunan Hausawa biyu a Ibadan sun tuɓe rawanin juna

Jayayyar jagorancin al’umma a tsakanin sarakunan Hausawan Ibadan da Sasa a Jihar Oyo ta fito da sabon salo, inda suka ayyana tuɓe rawanin juna mako biyu da suka gabata.

Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Ɗahiru Zungeru ne ya fara sanar da cewa ya tuɓe rawanin Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin a wajen taro da ’yan jarida a ranar 21 ga watan Oktoba a fadarsa da ke unguwar Sabo Ibadan.

Mako ɗaya bayan wannan sanarwa, Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihohi 17 a Kudancin ƙasa ta yi taro na musamman da ’yan jarida a Fadar Sasa, inda ita ma ta ayyana cewar, ta tuɓe rawanin Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Ɗahiru Zungeru.

Majalisar ta ce, a zaman da za ta yi nan gaba kaɗan za ta duba yiwuwar zuwa kotu a kan wannan lamari domin warware wannan matsala da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin ’yan Arewa da ke zaune a wannan sashe na ƙasa.

Da yake ƙarin haske a wajen taron, Kakakin Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihohi 17 na Kudancin ƙasa, Sarkin Hausawan Amuwo-Odofin, Alhaji Sulaiman Rabi’u (JP) ya ce, “majalisarmu ba za ta taɓa amincewa da irin wannan surkulle da Sarkin Hausawan Ibadan da hakimansa suke yi ta fannin shiga cikin hurumin da ba na su ba.

Sun wuce gona da iri, shi ne dalilin ɗaukar matakin dakatar da Sarkin Hausawan Ibadan daga kiran kansa a matsayin sarki a dalilin irin kalaman da yake yi ga uban tafiya, Alhaji Haruna Maiyasin Sardaunan Yamma kuma Shugaban wannan majalisa a Jihohin Kudancin ƙasa baki ɗaya.”

Ya ce, “irin waɗannan kalamai za su iya janyo rikici da koma-bayan ci gaban miliyoyin ’yan Arewa mazauna wannan sashe na ƙasa.”

Shi kuwa Garkuwan Jihohin Yamma kuma Sarkin Bai na Jihar Legas, Alhaji Shehu ’Yarmusa cewa ya yi, “idan kun lura da yawan sarakunan Hausawa da Fulani da sarakunan samari da shugabannin ƙungiyoyin ’yan Arewa da suka yi wo tattaki daga wasu garuruwan Kudancin ƙasa zuwa wajen wannan taro, za ku gane cewa, akwai lauje cikin naɗi a kan kalaman da suke fitowa daga bakin Sarkin Hausawan na Ibadan.”

Ya ce, “akwai alamar sarkin Hausawan Ibadan ya jahilci yanayin zamantakewa da jagorancin al’umma kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Saboda haka muka gargaɗe shi cewa, ya iya bakinsa a kan kalaman da za su iya kawo rabuwar kawunan mutanenmu, musamman a irin wannan lokaci na tsadar rayuwa,’’ in ji shi.

Alhaji Shehu ’Yarmusa ya yi wa mahalarta taron tuni a kan matsayin Sardaunan Yamma, Alhaji Haruna Maiyasin da mahukunta tare da al’ummomi na ciki da wajen Nijeriya suke girmama shi a kan fafutukar samar da zama lafiya da ci -gaban jama’ar sa.

Ya ce, “wannan mutumi (Haruna Maiyasin) ya wuce raini, saboda haka bai kamata irin waɗannan mutane su fito da rana-tsaka ta hanyar yin amfani da kafofin watsa labarai domin cim ma mummunan buri ba. Ba za mu taɓa amincewa da hakan ba domin zama lafiya da kwanciyar hankali muke buƙata a ƙasa baki ɗaya,’’ in ji shi.

Sarkin Hausawan Ifon a Jihar Osun, Alhaji Sulaiman Muhammad da jagoran Shuwa-Arab a Jihohin Yamma, Sultan Ahmed Muhammad Magina da Zarmakwai na Jihohi 17 a Kudancin ƙasa, Alhaji Aliyu Abubakar da Sarkin Samarin Yamma, Alhaji Sani Salisu Ɗan Muttaƙa da Arɗon Arɗoɗin Yamma, Alhaji Yakubu Bello suna daga cikin manyan mutanen da suka tofa albarkarkacin bakinsu a wajen wannan taro.

Tun da farko sai da Ciroman Sarkin Sasa, Alhaji Ahmed Haruna Maiyasin ya karanta wa mahalarta taron wata wasiƙa a madadin Sardaunan Yamma Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihohi 17 na Kudancin ƙasa da ke cewa, “matakin cin zarafi da wulaƙanci da Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Ɗahiru Zungeru ya ɗauka abun dubawa ne saboda bai isa ya ce ya tuɓe min rawanin da Allah Ya ɗora min da mahukuntan ƙasa da al’ummar waɗannan jihohin suka zartas da hakan ba.”

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa