Sarakunan Hausawa sun jinjina wa mahukunta kan matakan tabbatar da tsaro

“Za mu iya cim ma wannan buri ne idan sarakunan Hausawan da shugabannin ƙungiyoyi da malamanmu suka haɗa kai.

Sarakunan Hausawa sun jinjina wa mahukunta kan matakan tabbatar da tsaro

Sarakunan Hausawa a garuruwa fiye da 30 a jihohin Kudu maso Yammacin Nijeriya sun nuna yaba da matakan da Gwamnatin Tarayya da jihohi suke ɗauka wajen daƙile matsalolin tsaro a ƙasa baki ɗaya.

Sun nemi ’yan Nijeriya su bayar da gudunmawarsu ga shirin tsaron ƙasa musamman ta fannin bayar da bayanan sirri da za su kai ga bankaɗo miyagu.

Sarakunan sun jagoranci jama’arsu ne zuwa wajen ɗaurin auren ɗan Sarkin Hausawan Ore, Alhaji Abdullahi Bagobiri, a ranar Lahadi a garin na Ore a Jihar Ondo.

Sarkin Hausawan Shasha Akure, ya shaida wa Aminiya cewa a taron shekara shekarar, “za mu riƙa tattauna matsalolin zamantakewa a tsakanin jama’armu da al’ummomin Yarbawa a garuruwa daban­daban a wannan sashe.

“Haka kuma, irin wannan taro ne zai taimaka mana wajen lalubo hanyar tafiya da murya ɗaya domin fafutukar neman haƙƙinmu da kusantar gwamnatocin waɗannan jihohin domin samun tallafin guraben karatu ga ’ya’yanmu da samun guraben ayyuka idan sun kammala karatun da kuma samun tallafin kayan koyon sana’o’i ga matasan Hausawa.”

Ya ce, hakan zai samu ne idan sarakunan Hausawan suka haɗa kai suka jajirce tsakani da Allah domin fafutukar sauke nauyin amanar da ke kansu.

Ya ce, “za mu iya cim ma wannan buri ne idan sarakunan Hausawan da shugabannin ƙungiyoyi da malamanmu suka haɗa kai.

“Amma muddin muka ci gaba da irin wannan zama na son zuciya da rashin adalci, to kuwa babu inda za mu je sai baƙin cikin da za mu riƙa gani a kulluyaumin ta fannin danne haƙƙinmu a matsayin ’yan Nijeriya ba tare da samun waɗanda za su iya shawo kan lamarin ba.”

Ya yi kira ga ’yan Arewa su ci gaba da haƙuri da girmama doka da oda tare da kyautata zamantakewa a tsakaninsu da jama’ar garuruwan da suke zaune a wannan.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa