Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba

Ba za mu bari wasu maƙiya su tauye wa al’ummar Kano wannan haƙƙin da suke matuƙar mutuntawa ba.

Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya umarci ɗaukacin Masarautun Kano guda huɗu da su fara shirye-shiryen Hawan Sallah da bisa al’ada aka saba domin ganin jama’a da maziyarta sun nishaɗantu a yayin bukukuwan Sallah na bana.

Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a yayin wani taron buɗa-baki da sarakunan gargajiya da aka yi a ɗakin taro na Ante Chamber da ke gidan gwamnatin Kano a ranar Talata.

Abba ya jaddada cewa al’ummar jihar sun ƙagara don ganin wannan al’ada ta sanya sabbin tufafi a lokacin bukukuwan Sallah, tare da tsayawa a kan tituna domin kallon sarakunansu a kan doki suna musayar gaisuwa.

“Al’ummar Kano babu abin da suke a duniya, illa bayan azumin watan Ramadan, su caɓa ado, su fito su yi dandazo a bakin titi, sarkinsu ya fito, hakimai su fito a kan dawakai, su yi jinjina su yi godiya, sannan sarki ya yi musu addu’a.”

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba, kuma ba za ta bari wasu maƙiya su tauye wa al’ummar wannan haƙƙin da suke matuƙar mutuntawa ba.

Kazalika, ya tabbatar da cewa dukkanin hukumomin tsaro a jihar za su ba da himma wajen bai wa jama’a kariya a yayin bukukuwan.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa za a ƙaddamar da Majalisar Masarautar Jihar Kano a watan Afrilun bana domin samun damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa za a sanar da ka’idoji, tsare-tsare da sauran muhimman abubuwan da suka danganci majalisar a ranar ƙaddamarwa.

Ya yaba wa sarakunan bisa kyakkyawar alaƙar da suka nuna tun bayan naɗa su, inda ya ce wannan shi ne karo na farko a tarihin jihar da ake samun mutuntawa a tsakanin sarakunan musamman ta fuskar matsayi.

A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Masarautar Kano kuma Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, ya tabbatar da cewa alaƙar da ke tsakaninsa da sarakunan ta musamman ce.

Ya yi kira ga Gwamnan da ya yi amfani da masarautun gargajiya wajen yaɗa manufofi da tsare-tsare ga al’umma, tare da tabbatar da aiwatar da ayyuka cikin inganci.

A nasu ɓangaren, Sarkin Karaye, Muhammad Muhammad Maharaz; Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umaru; da mai martaba Sarkin Gaya Dokta Aliyu Ibrahim Abdulkadir duk a madadin jama’arsu, sun yaba wa Gwamnan kan samar da takin zamani da sauran ababen more rayuwa a fannonin ilimi, lafiya da tituna a yankunansu.

Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah

Gobara ta kashe yara 3, ta jikkata 13 a Yobe

Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas

Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira