Sarakunan kasashen Benin da Kamaru sun koka kan rufe iyakokin Najeriya
Sarakunan gargajiya na kasashen Kamaru da Benin sun koka bisa matakin da mahukutan Najeriya sukia dauka na rufe iyakokin kasar nan inda suka ce, hakan na zama barazana ga ’yan uwantakan da ke tsakanin kasashen da Najeriya. A taron da sarakunan suka yi a makon jiya a yankin Dahe da ke kasar Benin sun mayar […]
Sarakunan gargajiya na kasashen Kamaru da Benin sun koka bisa matakin da mahukutan Najeriya sukia dauka na rufe iyakokin kasar nan inda suka ce, hakan na zama barazana ga ’yan uwantakan da ke tsakanin kasashen da Najeriya.
A taron da sarakunan suka yi a makon jiya a yankin Dahe da ke kasar Benin sun mayar da hankali sosai kan rufe iyakokin Najeriya da ake ci gaba da yi, inda suka ce akwai bukatar hadin kai a tsakanin daukacin shugabannin gargajiya na Afirka domin magance matsalar.
Shugaban Majalisar Sarakunan da suka halarci taron Farfesa Octabe Hudagbe, wanda shi ne babban basaraken Lardin Dahe a kasar Benin ya shaida wa Aminiya cewa, tsamin dangantakar da ke tsakanin Najeriya da kasar Benin abu ne mai sauki da za a iya magance shi inda akwai hadin kai a tsakanin sarakunan gargajiyar kasashen biyu. Ya ce Turawan mulkin mallaka ne suka zubar da mutunci da daraja tare da kyamar sarakunan gargajiya lamarin da ya sanya ake ganin ba za su iya tabuka komai ba, “Amma tasirin sarakunan gargajiya wajen magance matsaloli ba kadan ba ne,” inji shi.
Haka zalika basaraken Lardin Batoke da ke kasar Kamaru, Cif Molabie Otto, ya shaida wa Aminiya cewa matakin na gwamnatin Najeriya ya jefa al’ummar kasashen cikin wani hali, “Wannan abu ya taba mu ta kowane hali, al’umma na jin jiki, duk da ana alakanta wannan mataki da sha’anin tsaro to ya kamata a sani sarakunan gargajiya su suka fi kusa da al’umma idan za a yi aiki da su za su magance matsalolin ba tare da an kai ga daukar matakin rufe kan iyaka ba. Domin yin hakan barazana ce ga ’yan uwantakar da ke tsakanin kasashen Afirka,” inji shi.
A karshe sarakunan sun karrama Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya da lambar yabo ta girmamawa lura da yadda ya ke sanya sarakunan gargajiyar kasarsa a al’amuran gudanarwa na jagoranci a Kamaru, inda suka ce za su ci gaba da gwagwarmaya har sai an samu irin haka a ragowar kasashen Afirka.