‘Sarakunan Katsina na taimaka wa ‘yan bindiga’
Fadar Shugaban Kasa ta zargi sarakunan gargajiya a Jihar Katsina da hada baki da ‘yan bindiga da ke kai hare-hare a jihar. Babban Hadimin Shugaba Kasa kan Yada Labarai Garba Shehu ya ce sarakunan na taimaka wa maharan su tsere kafin sojoji su kai musu hari. “Hatta a jihar Katsina inda Shugaban Kasa ya fito, […]
Fadar Shugaban Kasa ta zargi sarakunan gargajiya a Jihar Katsina da hada baki da ‘yan bindiga da ke kai hare-hare a jihar.
Babban Hadimin Shugaba Kasa kan Yada Labarai Garba Shehu ya ce sarakunan na taimaka wa maharan su tsere kafin sojoji su kai musu hari.
“Hatta a jihar Katsina inda Shugaban Kasa ya fito, an sami wasu sarakuna da ke hada baki da ‘yan fashin daji a cutar da mutanensu”, in ji shi.
‘Yan bindiga na yawan kai hare-hare a yankunan jihar Katsina musamman a makon jiya, inda suka kashe kusan mutum 100 a kauyuka.
- ‘Yan bindiga: Gwamnati ta gaza —Gwamnan Katsina
- ‘Yan bindiga sun kara kashe basarake a Katsina
- Mutum 60 ‘yan bindiga suka kashe a Katsina — Mazauna
A hirarsa da gidan talbijin na Channels a ranar Litinin inda ya ce miyagu na amfana da ayyukan ‘yan bindigar, Garba Shehu ya ce, “A jihar Zamfara ma sai da aka tube wasu Sarakuna da hakimai”.
Jami’in ya ce a baya lokacin da abin ya fi kamari a jihar Zamfara, kafin jiragen yaki da aka girke a Katsina su kai wa ‘yan bindiga hari wasu sun kira sun sanar da su har sun sake wurin buya kafin jiragen su isa.
Ya ce, “Karshenta dole jiragen suka koma tashi daga Kano da Kaduna domin kai wa ‘yan bindiga hari a Zamfara”.
Garba Shehu ya yi kira da a taimaka wa gwamnati ta hanyar bayar da bayanai da za su taimaka wajen magance ayyukan maharan.
“A matsayinmu na ‘yan kasa akwai hakki a kanmu na mu taimaka wa sojoji da bayanai”, inji shi.