Sarakunan Kudancin Kaduna sun yaba wa El-Rufa’i kan sake bude makarantu
Sarakunan Kudancin Jihar Kaduna sun ziyarci Gwamnan Jihar Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i domin yi masa godiya kan sake bude manyan makarantun da suke yankin. A watannin baya ne gwamnatin jihar ta ba da umarnin rufe manyan makarantun da suke Kudancin Jihar saboda yawan tashe-rashen hankali da ake yi a yankin. A makon jiya ne Gwamna […]

Sarakunan Kudancin Jihar Kaduna sun ziyarci Gwamnan Jihar Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i domin yi masa godiya kan sake bude manyan makarantun da suke yankin.
A watannin baya ne gwamnatin jihar ta ba da umarnin rufe manyan makarantun da suke Kudancin Jihar saboda yawan tashe-rashen hankali da ake yi a yankin.
A makon jiya ne Gwamna El-Rufa’i ya ba da umarnin bude makarantun da suka hada da Kwalejin Ilimi da ke Gidan Waya da Jami’ar Jihar Kaduna da ke Kafanchan.
Da yake jawabi a gaban Gwamnan, Mai martaba Sarkin Jema’a Alhaji Muhammadu Isa Muhammad ya ce sun yanke shawarar zuwa wurin Gwamnan ne domin yin godiya gare shi kan sake bude makarantun. Ya ce yin haka zai taimaka matuka wajen bai wa dalibai damar ci gaba da neman iliminsu. “Muna godiya ga Allah kuma muna godiya Gwamnan saboda nasarar da aka samu wajen maido da zaman lafiya a Kudancin Jihar nan. Hakika Gwamna ya taka rawar gani sosai wajen ganin mun samu zaman lafiya. Har ila yau muna sake nuna farin cikinmu da godiya ga Allah da Ya dawo mana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari gida lafiya,” inji Sarkin.
Da yake mayar da jawabi, Gwamna El-Rufa’i ya ce hakika gwamnatinsa ta dauki matakin rufe makarantun ne da kyakkyawan nufi ba kamar yadda wadansu suke korafi ba. “Wadansu suna cewa wai mun rufe makarantun ne domin hana yara karatu a Kudancin Kaduna wanda hakan ba gaskiya ba ne. Matakin da muka dauka mun yi shi ne da kyakkyawar niyya. Burinmu shi ne kare rayukan yaranmu da ke karatu a can. Saboda haka bayan mun gamsu da zaman lafiyar yankin sai muka ga ya dace mu sake bude makarantun,” inji Gwamnan.
Gwamna El-Rufai ya kuma gode wa sarakunan Kudancin Kaduna kan goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa da kuma zaman lafiyar Kudancin Jihar.