Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Tawagar ta bayyana irin alaƙar da ke tsakanin Nijar da Jihar Yobe.

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Tawagar Sarakunan Gargajiya daga Jamhuriyar Nijar, ta jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Yobe kan ambaliyar ruwa da kisan gillar  Mafa, wanda ya kai salwantar rayuka da dukiyoyi.

Cikin waɗanda suka kai ziyarar jajen, sun haɗa da shugaban tawagar Mai Martaba Sarkin Maine-Soroa, Abdou Katielou Katiella Gasso, wanda ya ce, a matsayinsu na maƙwabta nagari, ya zama wajibi su nuna alhininsu dangane da wannan Iftila’in da Jihar Yobe ta samu kanta.

Ya ce al’ummar Yobe da Jamhuriyar Nijar suna da alaƙa ta hanyar al’adu, addini, da auratayya.

“Don haka abin da ya shafi ɗaya, yana shafar ɗaya kai-tsaye.”

Gwamnan Jihar Mai Mala Buni, ya yaba wa sarakunan bisa ziyarar sa suka kai wa jihar.

“Ina yaba muku da kiyaye alaƙar gargajiya a tsakanin mutanenmu, hakan zai ƙarfafa tare da inganta alaƙar da muke da ita tun fil-azal,” in ji shi.

Zaɓen Edo: Yadda aka kama masu sayen ƙuri’a da ’yan daba

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina