Sarakunan Zamfara sun fitar da sunayen da sojoji suka kashe

Majalisar sarakunan jihar Zamfara ta maida martanin akan zargin da rundunar sojan sama tayi, inda ta fitar da jerin sunayen fararen hula 11 da jirgin yakin rundunar ya hallaka a wani hari aka kaddamar a wasu yankunan karkara a jihar. Majalisar ta bayyana sunayen nasu kamar haka, Mai Daji Barau, Na Dumburum, Suwaiba Alka, `Yar […]

Sarakunan Zamfara sun fitar da sunayen da sojoji suka kashe

Sojojin saman Najeriya

Majalisar sarakunan jihar Zamfara ta maida martanin akan zargin da rundunar sojan sama tayi, inda ta fitar da jerin sunayen fararen hula 11 da jirgin yakin rundunar ya hallaka a wani hari aka kaddamar a wasu yankunan karkara a jihar.

Majalisar ta bayyana sunayen nasu kamar haka, Mai Daji Barau, Na Dumburum, Suwaiba Alka, `Yar Guru Na Dumburum, Maryam Shafiu, Dahe Malan Sule, Buhari dan Kurma, Zaliha na Dumburum, Aisha Akilu, Alamin Alka da Fati ‘Yar Gum.

Bayan mutum 11 da aka kashe, wasu da dama sun jikkata a wani hari da jirgin ya kai a kauyen Dumburum da ke yankin karamar hukumar Zurmi, an kai wannan hari a ranar 9 ga watan Afrilu 2019, inda majalisar ta fitar da sunayen wadanda aka raunata, kamar haka: Haruna Kusu, Muhammad M Sani, Abdulrazak Abubakar,  Yakubu Yunusa, Dan Diyya, Sa’a Dayyabu, Yar’wargi Mamman, Gwamna Na Dumburum, Rashida Alka, Maryam Akilu da Sadiq Sukuranu. Haka kuma harin ya raba mutum 20 da gidajensu.