Saratu Gidado ta amarce

A ranar Asabar da ta gabata ne aka daura auren jarumar fina-finan Hausa Saratu Gidado (Daso) da Muhammad Auwal.An daura auren ne a unguwar Chiranci da ke Kano kusa da fadar Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, da misalin karfe 10:00 na safe a kan sadaki Naira dubu 30.Wata majiya ta shaida wa Aminiya angon mutumin […]

Saratu Gidado ta amarce
Saratu Gidado ta amarce

A ranar Asabar da ta gabata ne aka daura auren jarumar fina-finan Hausa Saratu Gidado (Daso) da Muhammad Auwal.
An daura auren ne a unguwar Chiranci da ke Kano kusa da fadar Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, da misalin karfe 10:00 na safe a kan sadaki Naira dubu 30.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya angon mutumin Damagaran ne ta kasar Nijar.
Binciken Aminiya ya gano ba kamar auren jarumar na farko ba, inda ‘yan fim suka yi dandazo, a wannan karon ‘yan fim kalilan ne suka halarci daurin auren wadanda suka hada da Gatari da Ahmad Tage da Baba Ari da sauransu.
Majiyarmu ta ruwaito cewa rashin halartar ‘yan fim da yawa daurin auren jarumar wacce a kwanakin baya ta samu sarautar Jakadiyar dan Majen Kano, wato Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Malam Sanusi Lamido Sanusi, ya kasance ne saboda boye batun auren da ta yi, wanda ake zaton ta yi hakan ne don gudun surutun jama’a, ganin cewa ba a dauki tsawon lokaci ba tsakanin aurenta na farko da kuma na biyun ba.
Jarumar za ta tare a gidan mijinta da ke Kano, sannan za ta ci gaba da fim.